Dakta Jamil Isyaku Gwamna, Sardaunan Gombe, ya kasance mutum da ke gudanar da jagoranci ta hanyar nuna misali da Shi kansa a dukkannin harkokinsa na jagorancin al’umma.
A lokacin da yake riƙe da muƙamin Manajan Darakta/Shugaban Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), ya nuna salon shugabanci mai kusanci da jama’a tare da ɗaukar matakai kai tsaye wajen magance matsaloli.,
Wannan muhimmin bayanin yana kunshe ne cikin wata sanarwar da kungiyar masu yada labarai Na Sardauna media team suka fitar, Akan kyawawan halayen Dr Jamil Isyaku Gwamna.
Duk lokacin da wata matsala ta taso, musamman wacce ta shafi al’umma, ba ya zama a ofishinsa ko ya dogara da rahotanni kaɗai ba. Maimakon haka, yakan kai ziyara da kansa zuwa yankunan da abin ya shafa domin ganin halin da ake ciki da idonsa tare da nemo mafita mai ɗorewa.
Wannan tsari nasa yana nuna shugabanci wanda ya ginu a kan gaskiya, riƙon amana, sa ido da kuma ɗaukar mataki cikin gaggawa a inda ya dace. Ya kasance kusa da jama’a, yana sauraron koke-kokensu tare da ɗaukar matakan rage musu wahala cikin lokaci.
Wannan shi ne alamar shugaba mai tausayi, wanda ya sadaukar da kansa wajen kyautata rayuwar jama’a tare da tabbatar da an samu sakamako mai amfani.
Kasancewarsa kusa da jama’a shi ne ginshiƙin shugabanci nagari kuma mai tasiri, domin ta nan ne, shugaba ke iya fahimtar halin da al’ummarsa ke ciki.
Idan aka ba shi damar jagorantar Jihar Gombe a matsayin Gwamna, akwai kyakkyawan fata cewa zai ci gaba da wannan salon shugabanci wanda ya ginu a kan kusantar jama’a, da riko da gaskiya da ƙwazo wajen aiki.
Jihar Gombe na buƙatar shugaba mai kuzari, Adalci, Amana, Gogewa, Sanin makamar aiki, Saurin amsa buƙatun jama’a, kuma mai alaƙa da talakawa Kai tsaye kamar yadda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya yake.
Irin wannan nagartar shugabanci ta bayyana a fili a cikin salon jagorancin Sardaunan Gombe, Dakta Jamil Isyaku Gwamna.
Saboda haka, muna kira ga al’ummar Jihar Gombe da su mara wa wannan tafiya baya tare da ƙarfafa ta domin ciyar da jihar gaba zuwa makoma mafi alheri.
Sa Hannu:
Sardauna Media Team
14th May, 2026

