Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»Politics»Gwarzo Ya Bukaci Matasa da Mata a Kano Su Yi Rajistar Katin Zaɓe Ta Intanet Kafin Ranar 24 ga Yuli
    Politics

    Gwarzo Ya Bukaci Matasa da Mata a Kano Su Yi Rajistar Katin Zaɓe Ta Intanet Kafin Ranar 24 ga Yuli

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanJuly 11, 20263 Mins Read
    FB IMG 1783798040822
    FB IMG 1783798040822

    Dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar New Democratic Congress (NDC), Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi kira ga dukkan ‘yan ƙasa da suka cancanci yin rajistar zaɓe amma har yanzu ba su yi ba,

    Ya hori musamman matasa da mata, da su yi amfani da sabon tsarin rajistar zaɓe ta intanet na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), su yi rajista daga gidajensu ta amfani da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) kafin wa’adin ranar 24 ga Yuli, 2026.

    Read also: Governor Radda Assures APC Northwest Reconciliation Committee of Party Unity

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Asabar, Kwamared Gwarzo ya bayyana cewa INEC ta ƙaddamar da sabon dandalin rajistar kai tsaye ta intanet, wanda ke bai wa masu yin rajista karo na farko damar fara da kammala rajistarsu ta hanyar shiga shafin cvr.inecnigeria.org.

    Ya jaddada cewa kaɗa ƙuri’a wata muhimmiyar hanya ce da ‘yan ƙasa ke bayyana ra’ayoyinsu tare da ba da gudunmawa wajen tsara makomar dimokuraɗiyyar ƙasa.

    A cewarsa “Wannan sabon tsari ya kawo ƙarshen wahalar tsayawa dogayen layuka. Yanzu matasanmu, iyaye mata da ‘yan’uwanmu mata za su iya yin rajista daga gida ta amfani da wayoyinsu ko kwamfutocinsu. Babu wani uzuri na rashin shiga cikin tsarin dimokuraɗiyya.”

    Gwarzo ya yi kira na musamman ga matasa da mata da su fito su yi rajista, yana mai jaddada cewa Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) shi ne babban makamin kawo sauyi mai kyau.

    Read also: GOV. LAWAL PLEDGES MORE PROJECTS AS APC CAMPAIGN STORMS SHINKAFI LGA

    Ya ce “PVC ɗinku shi ne ƙarfinku. Shi ne makamin da za mu yi amfani da shi wajen kawo sauyi mai kyau ga iyalanmu, al’ummominmu da kuma Jihar Kano baki ɗaya. Ina kira musamman ga matasa da mata—ku yi rajista, ku karɓi katin zaɓenku, sannan ku fito ku zaɓa a shekarar 2027.”

    Dan takarar na NDC ya kuma bukaci dukkan ‘yan Najeriya da suka cancanci yin rajista amma ba su yi ba da su kammala rajistarsu ta farko ta intanet, su je cibiyoyin da INEC ta tanada domin ɗaukar bayanan tantancewa (biometric), sannan su karɓi katin PVC ɗinsu da zarar an kammala.

    Ya ƙara da cewa “Makomar Jihar Kano da Najeriya tana hannun ‘yan ƙasa masu wayewa da ɗaukar alhakin da ya rataya a wuyansu. Ku yi rajista tun yanzu, ku fito ku yi zaɓe cikin lumana a shekarar 2027, domin tare mu gina Kano irin wadda muke buri.”

    Hakazalika, Gwarzo ya yi kira ga shugabannin al’umma, malamai da ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin fararen hula da su haɗa kai wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa su su yi rajistar zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

    Read also: Gov Inuwa Yahaya Flags off 12.7km Tudu Kwaya-Kuran Mota-Panguru Road, Commissions Billiri West LCDA Secretariat

     

     

    collect electorates gwarzo now pvc
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGwamna Charges Muslims to Deepen Qur’anic Education Among Children, Youth
    Next Article 2027: Your nomination is a confirmation of competence, loyalty, Speaker Abbas congratulates VP Shettima

    Related Posts

    Politics

    SHINKAFI RESIDENTS COMMEND GOVERNOR DAUDA LAWAL’S DEVELOPMENTAL STRIDES, PLEDGE SUPPORT FOR ALL APC CANDIDATES IN 2027

    November 28, 2026
    Politics

    Governor Radda Assures APC Northwest Reconciliation Committee of Party Unity

    November 28, 2026
    Politics

    GOV. LAWAL PLEDGES MORE PROJECTS AS APC CAMPAIGN STORMS SHINKAFI LGA

    November 27, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.