Ibrahim Sani shawai.
A daidai lokacin da siyasar Jihar Gombe ke ƙara ɗaukar hankali gabanin zaɓuɓɓukan gama gari na shekarar 2027, yana da matuƙar muhimmanci a wayar da kan al’umma, musamman matasa, game da tarihin wasu daga cikin ‘yan takara, irin gwagwarmayar da suka sha, da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban al’umma kafin zuwansu matakin da suke kai a yau.
Read also: GOMBE STATE IN FOCUS: We Have Reasons to Vote APC in Gombe State
Wannan maƙala tana mayar da hankali ne kan Dokta Jamil Isyaku Gwamna (Sardaunan Gombe), ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC—mutumin da tarihin rayuwarsa a siyasa ke nuna cewa, hakika: Sardauna ba sa’an yaro ba ne.
Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya fara harkokin siyasa tun a shekara ta 2000, lokacin da marigayi tsohon gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Habu Hashidu, ya gano basirarsa da jajircewarsa, inda ya ba shi muƙamin Shugaban Hukumar Kula da Samar da Ruwan Sha ta Jihar Gombe. Wannan muƙami ya zama wata babbar hanya da ta buɗe masa ƙofar shiga sahun gaba a siyasar Jihar Gombe. Tun daga wannan lokaci ya fara bayyana a matsayin matashi mai hangen nesa, mai kishin ci gaban jiharsa.
A ƙarƙashin mulkin Alhaji Abubakar Habu Hashidu, Dr. Gwamna ya kasance ɗaya daga cikin jiga-jigan gwamnati, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da mulki da tsara manufofin ci gaban jihar ta Gombe.
Har ila yau, yana cikin sahun gaba wajen goyon bayan yunƙurin neman wa’adi na biyu na gwamnan, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen shirya dabarun siyasa, wayar da kan al’umma da kuma haɗa kan jama’a. Wannan gogewa ta ƙara gina masa tubalin fahimtar siyasa da shugabanci.
Bayan wannan mataki, Dokta Gwamna ya ɗauki wani babban ƙalubale na neman shugabanci kai tsaye. A shekara ta 2007 ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP. Duk da cewa bai samu nasarar lashe zaɓe ba, hakan bai karya masa gwiwa ba. Maimakon haka, ya ci gaba da gwagwarmayar siyasa, yana ƙara kusantar al’umma tare da gina dangantaka da mu’amala da jama’a a matakin jiha da na ƙasa.
Sardaunan Gombe ya ci gaba da wannan gwagwarmaya har zuwa shekara ta 2019, lokacin da ya sake tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP. Wannan ma ya sake nuna jajircewarsa da ƙudurinsa na shugabantar Jihar Gombe.
Bayan zaɓen shekarar 2023, Dokta Gwamna ya koma jam’iyyar APC, inda a yau yake neman tikitin gwamna. Wannan tafiya mai cike da ƙalubale, haƙuri da juriya ta nuna cewa shi ba ɗan siyasar da ya shigo yau ko jiya ba ne. A maimakon haka, gogaggen ɗan siyasa ne da ya shafe kusan shekaru kusan talatin yana fafutukar siyasa.
Mafi akasarin Al’ummar Gombe na ganin cewa tsawon lokacin da ya shafe yana siyasa, gogewarsa a gwamnati, da kusancinsa da jama’a sun sanya shi a matsayin mafi cancanta da dacewa a cikin masu neman shugabancin Jihar Gombe a yanzu haka.
Baya ga siyasa, Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya yi fice wajen tallafa wa matasa, Maza da Mata da kuma marasa galihu. Ya kasance mai goyon bayan shirye-shiryen bunƙasa sana’o’in hannu, ba da horo ga matasa domin su dogara da kansu, tare da taimakawa wajen samar da ayyukan yi.
Haka kuma, ya tallafa wa mata ta hanyoyi daban-daban, ciki har da ƙarfafa musu gwiwa a harkokin kasuwanci da samar musu da hanyoyin samun kuɗin shiga. A tsawon shekarun da ya shafe yana siyasa, Al’ummar Jihar Gombe shaida ne cewa gudunmawarsa ta kai kusan kowane sashe da lungu na Jihar Gombe.
A fannin ci gaban ɗan Adam (Human Capital Development), Dokta Gwamna ya bayar da gudunmawa mai yawa. Ya tallafa wa ɗalibai ta hanyar taimakon karatu, ya kuma ƙarfafa harkokin ilimi da kiwon lafiya a matakai daban-daban. Wannan ya sa mutane da dama ke kallonsa a matsayin shugaba mai kishin jama’a, wanda ya fahimci cewa ci gaban al’umma yana farawa ne daga inganta rayuwar mutane, musamman matasa.
Dokta Jamil Gwamna, ya taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa sama da dubu ɗaya lokacin da yake Shugaban Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Gombe. Haka kuma, lokacin da yake shugabantar Kamfanin Rarraba hasken Wutar Lantarki na KEDCO, ya taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa sama da dubu ɗaya da ɗari biyar daga Jihar Gombe.
Bugu da ƙari, ya taimaka wa wasu matasa daga jihar wajen samun aiki a Kamfanin Rarraba hasken Wutar Lantarki na Kaduna (KAEDCO), wanda ke kula da jihohin Kaduna, Sokoto, Kebbi da Zamfara.
A fannin ilimi kuwa, ya ɗauki ɗalibai talatin da biyu daga Jihar Gombe zuwa Makarantar Sakandiren Kimiyya da Fasaha ta Yamusa da ke Jihar Kebbi. Haka kuma, ya taimaka wa wasu ɗalibai goma samun damar yin karatun digiri a ƙasar Morocco a fannoni daban-daban.
A bangaren ilimi, Dokta Jamil Isyaku Gwamna gogaggen masanin tattalin arziki ne. Digirinsa na farko, na biyu da na uku duk sun shafi tattalin arziki, kuɗi da harkokin kasuwanci.
A fannin addini kuma, DoktaJamil mahaddacin Alƙur’ani ne, kuma ya yi zurfin karatu a fannonin ilimin addinin Musulunci.
Ana iya auna ilimin mutum ta yadda yake amfani da shi wajen gudanar da rayuwarsa da mu’amalarsa da mutane a fannoni daban-daban.
Read also: Gombe Is APC, and APC Is Gombe
Jagoranci Mai Gina Mutane, Ba Siyasa Kawai Ba:
Idan aka yi nazari a kan rayuwar Dokta Jamil Isyaku Gwamna, za a fahimci cewa tafiyarsa ba ta tsaya ne kawai a neman mukami ba. A tsawon shekarun da ya shafe yana cikin harkokin gwamnati da siyasa, ya yi ƙoƙarin gina mutane ta hanyar ba su dama, ilimi, horo da kuma aikin yi. Wannan wata irin falsafa ce ta shugabanci wadda ke kallon ci gaban ɗan Adam a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma.
Masana harkokin shugabanci sun sha bayyana cewa shugaba nagari shi ne wanda zai kyautata rayuwar mutane fiye da yadda ya same su. Idan aka yi la’akari da irin matasan da suka amfana da guraben aiki, tallafin karatu, horon sana’o’i da sauran shirye-shiryen da ake dangantawa da Dokta Jamil Isyaku Gwamna, ana iya cewa ya yi ƙoƙarin gina al’umma tun kafin neman jagorancin jihar Gombe.
A siyasa, mutane da dama kan bayyana ne idan lokacin zaɓe ya yi. Amma akwai waɗanda al’umma suka riga suka sani ta hanyar ayyukansu na tsawon lokaci. A yanzu haka da yawa daga cikin Gwambawa na kallon Dokta Jamil Gwamna a matsayin ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane, saboda ya daɗe yana hulɗa da jama’a ba tare da la’akari da lokacin zaɓe ba.
Gogewar Gudanarwa da Fahimtar Tsarin Mulki:
Shugabancin jiha ba ya buƙatar farin jini kaɗai; yana buƙatar gogewa wajen tafiyar da manyan hukumomi, gudanar da ma’aikata, tsara kasafin kuɗi da yanke shawara cikin hikima ta hanyar amfani da Ilimi. Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya riƙe muƙamai daban-daban a matakin gwamnati da hukumomin gudanarwa masu zaman kansu, abin da ya ba shi damar fahimtar yadda gwamnati ke aiki ciki da wajen ta.
Wannan gogewa na iya zama wata kadara ga duk wanda yake son jagorantar jihar, domin shugabanci ba wai alkawura kawai ba ne, har da sanin yadda ake aiwatar da su cikin tsarin gwamnati.
Ɗorewa a Siyasa Alamar Juriya Ce:
Akwai ‘yan siyasar da sau ɗaya idan suka fuskanci rashin nasara sukan janye daga siyasa. Sai dai tarihin Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya nuna irin yadda tai tsayuwa irin ta daka tare da jajircewa wajen ci gaba da gwagwarmaya tsawon shekaru, duk da sauye-sauyen siyasa da kalubalen da ya fuskanta.
Ko mutum ya goyi bayansa ko bai goyi bayansa ba, abu ne mai wahala a musanta cewa ya kasance cikin fitattun ‘yan siyasar Jihar Gombe na tsawon lokaci. Wannan ɗorewa tana nuna haƙuri, juriya da kuma ƙudurin ci gaba da neman damar yi wa al’umma hidima.
Mu’amala Da Kowa Ba Tare da Bambanci Ba:
Ɗaya daga cikin siffofin shugabanci da ake yabawa ga Dokta Jamil Isyaku Gwamna shi ne yadda yake mu’amala da jama’a daga kowane mataki na rayuwa. Sarakuna, malamai, matasa, mata, ‘yan kasuwa da masu sana’o’i suna cikin waɗanda ya kasance yana hulɗa da su cikin girmamawa da mutuntawa.
A cikin al’umma mai bambancin ra’ayi da siyasa irin ta Jihar Gombe, irin wannan salon shugabanci na iya taimakawa wajen samar da haɗin kai da kwanciyar hankali da kuma zaman lafiya.
Hakika, tarihin Dokta Jamil Isyaku Gwamna na nuna juriya, ƙwarewa da sadaukar da kai wajen hidimtawa al’umma. Tafiyarsa tun daga shekara ta 2000 zuwa yau ta ƙunshi darussa masu yawa ga matasa masu sha’awar shiga siyasa, musamman darasin cewa siyasa tana buƙatar haƙuri, juriya da kishin jama’a.
Ba tare da wata shakka ba, a yanzu haka mafi akasarin Al’ummar Jihar Gombe na kallon Dokta Jamil Isyaku Gwamna a matsayin gogaggen ɗan siyasa wanda ya san tsarin shugabanci, ya fahimci buƙatun jama’a, kuma ya shafe shekaru masu yawa yana fafutukar hidimtawa al’ummar Jihar Gombe. Wannan ne ya sa suke cewa, hakika *Sardaunan Gombe ba sa’an yaro ba ne* a fagen siyasa da kuma harkokin gudanarwa na Mulki.
Ibrahim Sani Shawai
Mai Magana da yawun Dokta Jamil Isyaku Gwamna.

