Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Sarkin Gumel, Tare da Jinjinawa Shekaru 46 Na Mulkinsa
    News

    Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Sarkin Gumel, Tare da Jinjinawa Shekaru 46 Na Mulkinsa

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanSeptember 4, 20263 Mins Read
    FB IMG 1788505996528
    FB IMG 1788505996528

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Sarkin Gumel, Mai Martaba Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON, wanda ya rasu a ranar Alhamis, 3 ga Satumba, 2026, a birnin Alkahira na ƙasar Masar.

    A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Gumel, gwamnati da al’ummar Jihar Jigawa, da kuma daukacin masarautun gargajiya na Najeriya.

    Shugaban Ƙasan ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel a matsayin ƙarshen wani muhimmin tarihi, yana mai cewa marigayin ya hau gadon sarautar Gumel a ranar 16 ga Disamba, 1980, inda ya yi kusan shekaru 46 yana mulki a matsayin sarki na 16 na masarautar.

    Ya ce tsawon shekarun mulkinsa sun sanya marigayin cikin sarakunan gargajiya na farko da suka fi dadewa kan karagar mulki kuma suka fi samun girmamawa a Najeriya.

    Shugaba Tinubu ya kuma bayyana marigayin a matsayin ƙwararren malami, ma’aikacin gwamnati kuma ɗan kishin ƙasa, wanda gudummawarsa ga al’umma ta wuce iyakokin fada.

    Kafin ya zama sarki, Alhaji Ahmed Muhammad Sani II ya yi aiki a Hukumar Native Authority ta Gumel, Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, sannan ya kasance babban jami’i a Ofishin Gundumar Kazaure.

    Tsakanin shekarar 1978 zuwa 1980, ya kasance Kwamishinan Yaɗa Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu na tsohuwar Jihar Kano.

    A lokacin da yake wannan matsayi ne aka kafa jaridar Triumph Newspaper, tashar talabijin ta CTV 67 wadda daga baya ta zama ARTV, tare da faɗaɗa ayyukan Radio Kano. Wadannan kafafen yaɗa labarai na daga cikin muhimman cibiyoyin yaɗa bayanai a Arewacin Najeriya har zuwa yau.

    Shugaba Tinubu ya ce a lokacin da yake kan karagar sarautar Gumel, Alhaji Sani II ya sauya masarautar zuwa abin koyi wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.

    Ya bayyana shi a matsayin uba ga kowa, mai hikima da kuma mai kula da al’adun al’umma, wanda ya sadaukar da tsawon mulkinsa wajen inganta ilimi, karatun addinin Musulunci, haɗin kan al’ummomi daban-daban da kuma kare al’adun masarautar Gumel, wadda na daga cikin tsofaffin masarautun Arewacin Najeriya.

    Shugaban Ƙasan ya ce a Jihar Jigawa, salon jagorancin marigayin mai natsuwa, taka-tsantsan da kuma haɗa kan jama’a ya taimaka wajen samar da kwanciyar hankali a tsawon shekarun da jihar ta fuskanci sauye-sauyen siyasa da matsalolin tsaro.

    Ya ƙara da cewa marigayin ya kasance abokin hulɗa na gari wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma, tare da fifita jin daɗin jama’arsa a kan komai.

    Shugaba Tinubu ya ce Najeriya ta yi babban rashi na wani fitaccen shugaban gargajiya, wanda za a yi kewar shawarwarinsa masu hikima, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke ci gaba da dogaro da tasirin shugabannin gargajiya wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

    Shugaban Ƙasan ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya kuma ba shi Aljannar Firdausi.

    Ya kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalan marigayin, Masarautar Gumel da al’ummar Jihar Jigawa ƙarfin jure wannan babban rashi da baza a iya maye gurbinsa ba.

    emir gumel hausa mourn pbat
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleABU, Chinese varsity, AMA-MED sign pact on biomedical sciences, AI, others
    Next Article Zulum Seeks AfDB Partnership to Drive Borno’s Post-Conflict Recovery

    Related Posts

    News

    International Youth Day: Uba Sani Gives Financial Support To Innovators

    September 5, 2026
    News

    CORPS COMMANDER EDUCATION VISIT TO NAISET, NACOE…Commends Academic Excellence

    September 5, 2026
    News

    AN OPEN LETTER TO HIS EXCELLENCY, SENATOR UBA SANI, CON GOVERNOR OF KADUNA STATE SIR KASHIM IBRAHIM GOVERNMENT HOUSE, KADUNA

    September 5, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026295 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026242 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026226 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026168 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026165 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026156 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.