Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da ibadar Umrah da sanyin safiyar Juma’a a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, inda ya miƙa godiya ga Allah Madaukakin Sarki tare da roƙonSa da Ya ci gaba da jagorantar Nijeriya da kare al’ummarta.
A yayin ibadar, Shugaba Tinubu ya yi dawafi a ɗakin Ka’aba da ke cikin Masallacin Harami, yana mai bautar Allah, nuna godiya da roƙonSa bisa ni’imomin da Ya yi wa Najeriya da al’ummarta.
Read also: PRESIDENT TINUBU MOURNS FORMER LAGOS DEPUTY GOVERNOR SEN. IDIAT ADEBULE
Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala ibadar, Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa Umrah ɗin na da matuƙar muhimmanci wajen nuna ƙauna ga al’umma, jajircewa wajen gudanar da aiki da kishin ƙasa, tare da miƙa wuya ga ikon Allah.
Tinubu ya ce: “Na yi imanin cewa wannan Umrah tana da matuƙar muhimmanci wajen nuna ƙauna ga al’ummarmu, jajircewa wajen gudanar da aiki da kishin ƙasarmu Najeriya, da kuma bin abinda Allah ya fada cewa kalmarSa ita ce za ta yi rinjaye a dukkan komi. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, kuma Shi kaɗai ne ke ƙaddara abin da mutum zai kasance da abin da zai zama a rayuwarsa.”
Shugaban Ƙasar ya kuma roƙi Allah Ya azurta Najeriya da zaman lafiya mai ɗorewa, haɗin kan ƙasa, fahimtar juna da kwanciyar hankali. Ya kuma roƙi Allah Ya ba shugabannin ƙasar hikima, Ya ƙarfafa zumunci da ’yan’uwantaka tsakanin ’yan Najeriya, tare da kawo ƙarshen matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Read also: COAS JOINS PRESIDENT TINUBU, CDS, SERVICE CHIEFS IN PAYING LAST RESPECTS TO FALLEN NAF 931 CREW
“Ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar gudanar da wannan Umrah. Mun yi addu’a domin ƙasarmu, don kowa ya rayu cikin zaman lafiya, jituwa, farin ciki da imani da Allah Madaukakin Sarki,” in ji Shugaban Ƙasar.
Tinubu ya bayyana fatan Najeriya za ta ci gaba da samun ci gaba ta fuskar tattalin arziki, bunƙasar zamantakewa da inganta tsaro domin samar da kyakkyawar makoma ga dukkan ’yan ƙasar.
Ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na gina Najeriya mai zaman lafiya, haɗin kai da wadata, inda kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da addininsa ko asalinsa ba, zai rayu cikin tsaro, mutunci da jituwa.
Read also: Gwamna Commends Construction of 13 LCDA Secretariats, Pledges to Consolidate Gains
Sabuwar Nigeria.
