Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa al’ummar Jihar Rivers bisa irin goyon bayan da suka ba shi a zaɓen 2023, tare da neman ƙarin goyon bayansu a zaɓen 2027.
Da yake jawabi a babban taron kamfen na APC da aka gudanar a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, Shugaban Ƙasar ya yaba da yawan jama’ar da suka halarta, tare da jinjina wa sulhun da aka samu tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Read also: Court Affirms Lalong As APC Senatorial Candidate, Dismisses Lar’s Suit
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa Gwamna Fubara bisa nuna dattako da fahimta wajen amincewa da shawarwarin dattawan siyasa da suka taimaka wajen warware rikicin da ya tsakaninsa da magabacinsa.
A nasa jawabin, Gwamna Fubara ya yi alkawarin cewa Jihar Rivers za ta samar wa Shugaba Tinubu kuri’u miliyan uku a zaɓen 2027, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansa ga tafiyar Rainbow Coalition karkashin jagorancin Nyesom Wike.
Read also: A4A Elders More Relevant to Communities Than ACF Elders, Says Jadda Garko
Taron ya kuma haɗa magoya bayan APC da PDP, lamarin da ke nuna haɗin gwiwar ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a jihar domin goyon bayan takarar Shugaba Tinubu.
#ArewaforAsiwaju #A4A




