Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) kan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026, a cibiyar Super Dome da ke birnin Jeddah, inda
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Mataimakin Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Abdulfattah bin Sulaiman Mashat, ya sanya hannu a madadin ƙasarsa.
Read also: SNB KADUNA STATE CHAPTER CONGRATULATES PROF ADAMA ON HER ELEVATION TO PROFESSOR.
Yarjejeniyar ta tanadi tsarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu wajen tsara halartar alhazan Najeriya, rabon kujerun aikin Hajji, bin dokoki da ƙa’idojin Saudiyya da kuma kiyaye wa’adin kammala shirye-shirye. Haka kuma, za ta taimaka wajen inganta ayyukan masauki, sufuri da kiwon lafiya, tare da ƙarfafa sa ido kan ingancin hidimomin da ake ba alhazai da kuma kare lafiyarsu da jin daɗinsu.
Da yake jawabi a wajen bikin, Ambasada Ismail Abba Yusuf ya yaba wa gwamnatin Saudiyya da Ma’aikatar Hajji da Umrah bisa ci gaba da zuba jari wajen inganta kayayyakin more rayuwa da shirye-shiryen aikin Hajji. Ya kuma tabbatar da aniyar NAHCON na ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin Saudiyya domin inganta hidimomin da ake yi wa alhazan Najeriya. A nasa jawabin, Dr. Mashat ya bayyana cewa alhazan da suka gudanar da Hajjin 2026 sun nuna gamsuwa da ayyukan da aka yi musu da kashi 93 cikin 100, inda ya yaba wa Najeriya bisa gudunmawar da ta bayar wajen cimma wannan nasara. Ya kuma jinjinawa Najeriya bisa cika wa’adin shirye-shiryen Hajjin 2027, tare da buƙatar NAHCON ta ci gaba da wannan ƙoƙari.
Taron sanya hannu kan yarjejeniyar ya samu halartar Ambasadan Najeriya a Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo, da wasu mambobin Majalisar Tarayya ƙarƙashin jagorancin Hon. Jafar Mohammed, shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da aikin Hajji, da sauran manyan jami’ai. NAHCON ta bayyana cewa za ta yi aiki tare da hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohi, kamfanonin shirya aikin Hajji masu lasisi da hukumomin Saudiyya domin daidaita shirye-shirye, ƙarfafa sa ido kan hidimomi da magance matsalolin da ka iya tasowa kafin fara aikin Hajjin 2027.


