Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»Politics»Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro, ya gode wa al’ummar Jigawa kan goyon bayansu
    Politics

    Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro, ya gode wa al’ummar Jigawa kan goyon bayansu

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanNovember 11, 20263 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1794423878560

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya, tare da bayyana cewa gwamnatinsa na ƙara inganta walwala da albashin jami’an tsaro domin ƙarfafa musu gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani gangamin jam’iyyar APC a filin wasa na Dutse Township da ke jihar Jigawa, inda ya ce gwamnatinsa na ƙarfafa rundunar soji da ’yan sanda, tare da biyan su albashi mafi inganci. Ya kuma tabbatar da cewa Najeriya za ta yi nasara a kan makiyan zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.

    Shugaban ya gabatar da kundin manufofin APC mai taken “From Reforms to Prosperity”, wanda ya ƙunshi nasarorin gwamnatinsa da shirye-shiryen da take da su a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, noma da tsaro.

    Read also: GOV. LAWAL PLEDGES MORE PROJECTS AS APC CAMPAIGN STORMS SHINKAFI LGA

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shugaban Ya kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa kuɗaɗen da aka samu daga wannan mataki sun taimaka wajen gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa. Ya kuma yi alƙawarin ƙara tallafa wa manoman ƙananan gonaki ta hanyar samar musu da lamuni marasa ruwa, injinan noma da inganta hanyoyin ban ruwa domin tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.

    Read also: Campaign Train: Zulum Storms Mafa, Dikwa, Gamboru Ngala to Rousing Reception

    Kafin gudanar da gangamin, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da cibiyar koyon sana’o’i ta Bola Ahmed Tinubu Multi-Purpose Skills Acquisition Centre da Renewed Hope Technical Services Centre, sannan ya ƙaddamar da hanyar Old Police Station zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Dutse mai tsawon kilomita uku da aka mayar titin tagwaye. Haka kuma, ya ƙaddamar da taraktoci 400 da sauran kayan aikin gona da gwamnatin jihar ta saya domin bunƙasa noman zamani.

    A jawabinsa, Gwamna Umar Namadi ya gode wa Tinubu kan ayyukan raya ƙasa da tallafin da jihar ke samu, ciki har da aikin Greater Hadejia Water Project, kafa kwalejojin ilimi na tarayya a Dutse da Hadejia, shirin NELFUND da kuma tallafin Conditional Cash Transfer ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.

    Read also: MY GOV’T HAS PROJECTS WORTH ₦109 BILLION IN MARU LGA, GOV. LAWAL DECLARES DURING APC CAMPAIGN RALLY

    A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da sauran manyan jagororin APC sun buƙaci al’ummar Jigawa su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Tinubu, tare da zaɓen ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, na daga cikin manyan jiga-jigan da suka halarci gangamin, tare da gwamnoni, ministoci da sauran shugabannin siyasa daga sassan ƙasar nan. Tinubu ya kuma gode wa al’ummar Jigawa bisa goyon baya da biyayyarsu ga jam’iyyar APC.

    FB IMG
    FB IMG 1794423907770
    FB IMG
    FB IMG 1794423895947
    FB IMG
    FB IMG 1794423889020
    FB IMG
    FB IMG 1794423883603
    FB IMG
    FB IMG 1794423900253
    apce Jigawa pcc rally
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleIGP DISU CALLS FOR RESPONSIBLE REPORTING, STRONGER POLICE-MEDIA COLLABORATION AHEAD OF 2027 ELECTIONS
    Next Article POLICE ARREST SUSPECTED PHONES AND ACCESSORIES THIEF, RECOVER LAPTOP, 222 PHONES AND OTHER STOLEN GOODS FROM CITY CENTRE PLAZA

    Related Posts

    Politics

    Campaign Train: Zulum Storms Mafa, Dikwa, Gamboru Ngala to Rousing Reception

    November 28, 2026
    Politics

    MY GOV’T HAS PROJECTS WORTH ₦109 BILLION IN MARU LGA, GOV. LAWAL DECLARES DURING APC CAMPAIGN RALLY

    November 28, 2026
    Politics

    Kano Opposition Governorship Candidates Accuse APC, Incumbents Of Suppressing Dissenting Voices

    November 28, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.