Ƙungiyar Matazu Local Government Youth Development (MALGYD), bisa ƙudurin ta na bayar da gudummawa wajen tallafa wa matasa da bunƙasa rayuwar al’umma, ta gudanar da wani shiri na rabon tallafin kuɗi ga matasa maza da mata a ƙaramar hukumar Matazu.
An gudanar da wannan shiri ne a ƙarƙashin jagoranci da goyon bayan AA Mai Agogo Foundation, inda aka ware jimillar kuɗi har naira dubu ɗari da hamsin (₦150,000) domin tallafa wa mutum 50, inda kowannensu ya samu naira dubu uku (₦3,000).
Read also: Over 5,000 People Benefits From German Supported Project in Kaduna
An gudanar da wannan taro ne a babban ɗakin taron ƙaramar hukumar Matazu, tare da halartar manyan baƙi da suka haɗa da wakilin Shugaban Ƙaramar Hukumar Matazu, wakilin ɗan majalisar da ke wakiltar Musawa/Matazu Federal Constituency, wakilan ƙungiyar AA Mai Agogo APC Support Group Matazu, da sauran ƙungiyoyin matasa na ƙaramar hukumar.
Read also: Kukah Mourns Pete Edochie, Describes Him As Monumental Loss To Nigeria, Africa,
A yayin gudanar da taron, Shugaban ƙungiyar MALGYD ya bayyana godiya da jinjina ta musamman ga Mai Gida Alhaji Dr. AA Mai Agogo( Directorate contact and mobilization Tinubu/Dikko 2027 campaign),bisa irin gudummawa da kulawar da yake bai wa matasa da sauran al’umma, ba kawai a ƙaramar hukumar Matazu ba, har ma da sauran al’ummomin Jihar Katsina.
Haka kuma, ƙungiyar MALGYD ta sake jaddada goyon bayanta ga jam’iyyar APC daga sama har kasa a zabe mai gabatowa.
A ƙarshe, ƙungiyar MALGYD tana miƙa godiyarta ta musamman ga Mai Gida Dr. AA Mai Agogo(Directorate contact and mobilization Tinubu/Dikko 2027 campaign)bisa wannan karamci da goyon baya. Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya saka masa da mafificin alheri, Ya ƙara masa lafiya, arziki da ɗaukaka, Ya kuma albarkaci dukkan al’amuransa.
Haka kuma, muna addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a ƙaramar hukumar Matazu, Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.



