Shugaban Ƙaramar Hukumar Zariya, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad Jaga, a yau tare da Mai Girma Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, Ph.D., GCON, sun halarci ƙaddamar da rabon kayan wasanni ga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 200 daga cikin unguwanni 13 na Mazabar Tarayya ta Zariya.
Wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun Galadima Ishaq jamiin hulda da yan jarida a ofishin Shugaban karamar hukumar ta ce Kayan wasannin da Mai Girma Speaker ya samar sun haɗa da rigunan wasanni, rigunan atisaye, ƙwallaye, kayan atisayen masu horaswa da sauran muhimman kayayyakin wasanni, domin bunƙasa wasanni a matakin al’umma da kuma ƙarfafa matasa masu hazaka a fannin wasanni a faɗin mazabar.
Read also: Oversight: Speaker Abbas inspect some projects in his constituency.
Wannan shiri na daga cikin manyan ƙoƙarin Mai Girma Speaker na bunƙasa harkokin wasanni, waɗanda suka haɗa da gina filayen ƙwallon ƙafa guda huɗu masu ɗaukar ‘yan wasa biyar-biyar, gyarawa da sabunta manyan filayen wasanni guda huɗu, tare da ɗaukar nauyin mutane 21 domin samun ƙwararren horon koyar da wasanni a Cibiyar Horas da Masu Koyar da Wasanni ta Ƙasa (National Institute for Sports – NIS).
Sauran ayyukan da aka gudanar sun haɗa da gina babbar Cibiyar Horas da Ƙwararrun Wasanni (Sports Academy) a Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli, samar da sabon filin wasa a Ƙaramar Hukumar Lere, shirin gyara Filin Wasan Sabon Gari, da kuma cikakken aikin sabunta Filin Wasan Polo na Zariya.
Haka kuma, Mai Girma Speaker ya ɗauki nauyin gasar wasannin motsa jiki tsakanin makarantun sakandare a ƙananan hukumomi takwas na Shiyyar Kaduna ta Arewa (Zone One), tare da alƙawarin ci gaba da gudanar da gasar a duk shekara.
Bugu da ƙari, ana shirye-shiryen buɗe Makarantar Horas da Ƙwararrun Wasanni ta Teejay Foundation a watan Janairu na shekarar 2027. Makarantar, wadda za ta ƙunshi matakin firamare da sakandare, za ta samar da ilimi kyauta tare da ɗaukar cikakken nauyin karatun yara marasa galihu masu baiwar wasanni, tun daga matakin firamare har zuwa sakandare.
Bayan kammala bikin ƙaddamar da rabon kayan wasannin, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya kasance cikin tawagar Mai Girma Speaker da ta gudanar da rangadin duba ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a sassa daban-daban na Zariya.
Read also: Over 5,000 People Benefits From German Supported Project in Kaduna
Rangadin ya fara ne a Cibiyar Nazarin Fata da Fasahar Sarrafa Ta (Nigerian Institute of Leather and Science Technology – NILEST), inda suka duba yadda aikin gina ɗakin kwanan ɗalibai mai ɗaukar ɗalibai 320 ke gudana.
Daga nan, tawagar ta wuce Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli, inda ta duba manyan ayyuka guda huɗu da suka haɗa da Kwalejin Kimiyyar Dabbobi da Kiwo (College of Veterinary and Animal Science), Kwalejin Noma (College of Agriculture), Cibiyar Horas da Ƙwararrun Wasanni (Sports Academy), da Cibiyar Nazarin Gudanarwa (Centre for Management Studies).
Haka kuma, rangadin ya haɗa da duba Cibiyar Bunƙasa Mata da ke kusa da Filin Idi, Katsina Nawa; Cibiyar Bunƙasa Fasaha (Technology Incubation Centre) da ke Nagoyi; da kuma aikin gina makarantar firamare da sakandare ta musamman domin yara masu buƙata ta musamman, wadda ake ginawa a Banzazzau.
A yayin rangadin, an lura da yadda ayyukan ke ci gaba a wurare daban-daban. Waɗannan ayyuka na nuni da zuba jari mai yawa a fannonin ilimi, wasanni, bunƙasa ƙwarewar al’umma da ƙarfafa cibiyoyin ilimi, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a Zariya.
A cikin sauran harkokin ranar, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya kuma halarci ganawa da ɓangaren mata na ƙungiyar City Boy Movement, inda aka haɗu da shugabanninta da wakilai daga ƙananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna.
Read also: EXECUTIVE COUNCIL MEETING,ENGR JAGA CHAIRS 19 COUNCIL MEETING,FLAGS OFF NPC E-REGISTRATION IN ZARIA.
An kammala ayyukan ranar ne da wata ganawa da shugabannin addinai ƙarƙashin shirin Religious Leaders in Public Enlightenment and Community Engagement (RELPEACE). Tattaunawar ta mayar da hankali kan wayar da kan al’umma, ƙarfafa hulɗa da jama’a, da muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da cibiyoyin addini wajen tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaban al’umma.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya nuna godiya ga Mai Girma Speaker, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, Ph.D., GCON, bisa ci gaba da ayyukan raya ƙasa da yake samarwa a Zariya da sauran sassan Jihar Kaduna, tare da jaddada aniyar ci gaba da mara wa dukkan shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al’umma da samar da ci gaba ga dukkan al’umma.











