Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris Ya Bukaci Kafofin Yaɗa Labarai Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya
    News

    Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris Ya Bukaci Kafofin Yaɗa Labarai Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanOctober 22, 20265 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1792696817960

    Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya yi kira ga kafofin yaɗa labarai a Najeriya da su ƙara himma wajen tantance sahihancin labarai tare da guje wa yaɗa bayanan ƙarya da labaran da aka ƙawata don tayar da hankali, musamman yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

    Ministan ya yi wannan kiran ne ranar Alhamis a Abuja, yayin ƙaddamar da sabon tsarin haɗa sassan aikin jarida na kamfanin Media Trust Group, mai wallafa jaridar Daily Trust.

    Read also: Governor Inuwa Yahaya Tasks Journalists to Harness Technology Without Surrendering Core Functions

    Idris ya ce kafofin yaɗa labarai na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da cewa sahihan bayanai ne ke jagorantar rahotanni da sharhin da ake gabatarwa ga al’umma, ba son zuciya ko muradin siyasa ba.

    Ya bayyana cewa yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, za a samu ƙaruwar saƙonnin siyasa, zarge-zarge da martani tsakanin masu ruwa da tsaki, lamarin da ke buƙatar ’yan jarida su riƙa bincika sahihancin duk wani bayani kafin yaɗa shi.

    Ya ce, “Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen 2027, nauyin da ke kan kafofin yaɗa labarai zai ƙara girma.”

    Ministan ya yi gargaɗin cewa bai kamata kafofin yaɗa labarai su fifita saurin fitar da labari ko jan hankalin masu karatu a kan sahihancin labari ba, yana mai cewa irin wannan ɗabi’a na iya jawo asarar amincewar da jama’a suke da ita ga kafafen.

    Ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin aikin jarida da suka haɗa da adalci, gaskiya, bayyana bayanai yadda suke da kuma bambance ra’ayi da sahihin labari.

    Idris ya kuma yi gargaɗin cewa wasu ’yan cikin gida da na ƙasashen waje na iya amfani da lokacin siyasa wajen yaɗa bayanan ƙarya da za su iya haddasa rashin fahimta da barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

    Saboda haka, ya buƙaci hukumomin yaɗa labarai su zuba jari wajen horas da ma’aikatansu tare da samar musu da kayan aikin tantance sahihancin bayanai. Ya kuma bukaci kafafen da su riƙa haɗin gwiwa wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, duk da gasar da ke tsakaninsu.

    Ministan ya ce bunƙasar fasahar (AI), da suka haɗa da hotunan bogi da bidiyoyin da aka ƙirƙira ko sauya wa, sun ƙara wahalar da aikin tantance sahihancin bayanai.

    Ya bayyana cewa sahihancin bayanan da jama’a suke samu zai taka muhimmiyar rawa wajen gina amincewa da tsarin dimokuraɗiyya.

    Read also: SPEAKER ABBAS TO YOUTHS, THE ROAD TO 2027 MUST LEAVE NO ONE BEHIND!

    Ya ce gwamnatin tarayya na ƙarfafa shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan yadda za su tantance bayanan da suke samu, ciki har da ƙoƙarin da ya taimaka wajen kafa Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta Wayar da Kan Jama’a kan Kafofin Yaɗa Labarai da Bayanai ta UNESCO, mai matsayi na 2, a Abuja.

    Ya ƙara da cewa gwamnati na kuma tattaunawa kan yadda za a yi amfani da fasahar AI cikin tsari da ɗaukar matakan da suka dace a harkar yaɗa labarai.

    Idris ya sake jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kallon kafofin yaɗa labarai a matsayin abokan hulɗa masu muhimmanci wajen ci gaban ƙasa da inganta dimokuraɗiyya.

    Ya ce gwamnati na goyon bayan ’yancin aikin jarida da kuma rawar da ’yan jarida suke takawa wajen bincikar ayyukan hukumomin gwamnati da tambayar masu riƙe da madafun iko.

    Sai dai ya bayyana cewa ya kamata a haɗa ’yancin aikin jarida da samar da hanyoyin da za su tabbatar da dorewar tattalin arzikin kamfanonin yaɗa labarai, yana mai cewa aikin jarida ba hidima ga al’umma kaɗai ba ne, har ma da sana’ar da ke samar da ayyukan yi da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin ƙasa.

    Da yake magana kan sabon tsarin aikin jarida na Media Trust Group, ministan ya ce matakin ya nuna yadda kamfanin ke ƙoƙarin dacewa da sauye-sauyen da ke faruwa a harkar yaɗa labarai, inda jama’a ke buƙatar sahihan bayanai ta jaridu, rediyo, talabijin da kafafen intanet.

    Ya taya shugabanci da ma’aikatan kamfanin murna bisa wannan ƙoƙari, tare da ƙarfafa musu gwiwar mayar da sabon tsarin cibiyar ƙirƙira, binciken zurfi da yaɗa labarai bisa ƙa’idojin aikin.

    Ministan ya kuma buƙaci kafofin yaɗa labarai su riƙa ba da kulawa ga labaran nasarori da abubuwan alheri da ke faruwa a Najeriya, ba wai mayar da hankali kan matsaloli da gazawa kawai ba.

    Ya ce bai kamata a ɗauki aikin jarida a matsayin sana’ar adawa da gwamnati a kowane lokaci ba, domin labaran abubuwan da ke tafiya yadda ya kamata su ma sun cancanci kulawa kamar yadda ake ba rahotannin gazawa da matsaloli.

    Read also: 2027: Speaker Abbas proposes PBAT Stewardship Account, seeks President Tinubu’s endorsement

    Ya buƙaci ’yan jarida su ci gaba da kare ’yancin aikinsu tare da bayar da gudummawa wajen samar da sahihin bayani da ci gaban ƙasa.

    Manyan baƙin da suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin; Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi; da Darakta-Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa, da sauran manyan baƙi da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai.

    FB IMG
    FB IMG 1792696843119
    FB IMG
    FB IMG 1792696832802
    FB IMG
    FB IMG 1792696827650
    FB IMG
    FB IMG 1792696822414
    FB IMG
    FB IMG 1792696790433
    FB IMG
    FB IMG 1792696798920
    FB IMG
    FB IMG 1792696804457
    FB IMG
    FB IMG 1792696809271
    info launched minister model newsroom trust
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGovernor Inuwa Yahaya Tasks Journalists to Harness Technology Without Surrendering Core Functions
    Next Article Gov Radda Announces School Fee Support for 100 Muduru Students

    Related Posts

    News

    GOV. DAUDA LAWAL SWEARS IN FIVE NEW PERMANENT SECRETARIES, CALLS FOR COMPLIANCE WITH PUBLIC SERVICE RULES

    October 22, 2026
    News

    *SNB KADUNA STATE CHAPTER CONDEMNS ARREST AND IMPRISONMENT OF KADUNA JOURNALIST, CALLS FOR RESPECT FOR PRESS FREEDOM*

    October 22, 2026
    News

    DG PCC SENATOR ABDULAZIZ YARI AND HIS TEAM VISITS EMIR OF ZAZZAU AMB AHMED NUHU BAMALLI

    October 22, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026381 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026354 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026262 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026252 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026196 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026179 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.