Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su guji halin ko-in-kula da zaɓe, da sayar da ƙuri’u, da kuma tashin hankali a lokacin zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Idris ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin ƙaddamar da gangamin wayar da kan al’umma da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ta fara a faɗin ƙasar domin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Read also: Gov. Yusuf Condoles Umar Farouk Yola over Wife’s Death
Ya ce zaɓe yana bai wa ’yan ƙasa damar zaɓar wakilan su da kuma taka rawa wajen tsara makomar ƙasar, yana mai gargaɗin cewa rashin shiga harkokin zaɓe, sayar da ƙuri’u da tashin hankali na raunana dimokiraɗiyya.
Ya ce: “Idan masu kaɗa ƙuri’a suka ƙaurace wa zaɓe, suka sayar da ƙuri’un su ko suka tada hankali, hakan na raunana tsarin dimokiraɗiyya baki ɗaya.”
Idris ya ce Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya a Nijeriya ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Read also: Governor Radda Bags 2026 GovTech Public Service Award, Dedicates Honour to Katsina People
Ya yi nuni da Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ya ce ta kawo sauye-sauye domin inganta gaskiya da riƙon amana, tare da ƙara amincewar jama’a da zaɓe.
Ministan ya yaba wa Darakta-Janar na NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, da ma’aikatan hukumar bisa ƙaddamar da gangamin, yana mai jaddada cewa nasarar sa za ta dogara ne da haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, hukumomin zaɓe, jami’an tsaro, shugabannin al’umma da kuma ’yan ƙasa.
Issa-Onilu ya ce NOA za ta yi amfani da ofisoshin ta da ke jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, wajen isar da saƙonnin gangamin zuwa ga al’umma ta hanyar amfani da harsunan gida, shirye-shiryen rediyo, tattaunawa da jama’a, wasan kwaikwayo da kuma kafafen sadarwa na zamani.
Ya ce gangamin zai ƙarfafa jama’a su shiga zaɓe, ya hana sayen ƙuri’u da tashin hankali a lokacin zaɓe, tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin yaɗa sahihan bayanai yadda ya kamata.
Read also: Gov. Radda Hosts Ex- Administrators, Education Secretaries from 34 LGAs
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya sake jaddada aniyar hukumar ta gudanar da sahihin zaɓe da zai bai wa kowa dama. Ya ce cimma wannan buri yana buƙatar fara shirye-shirye tun da wuri, haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da kuma shigar jama’a cikin harkokin zaɓe.
Manufar gangamin ita ce shawartar ’yan Nijeriya su yi zaɓen 2027 yadda ya kamata, su mutunta zaɓin wasu, tare da ƙin duk wani mataki da zai jefa rayuka cikin haɗari, ya kawo barazana ga haɗin kan ƙasa ko ya raunana dimokiraɗiyya.






