● Gangamin TMGA 2027 ya faɗaɗa zuwa Yobe bayan babban taron da aka gudanar a Yola, Adamawa
Dubun-dubatar magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne suka yi tattaki a birnin Damaturu, babban birnin jihar Yobe, domin nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasar da kuma aniyarsa ta neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027, ƙarƙashin inuwar gangamin Tinubu Must Go Again 2027 (TMGA 2027).
Read also: Campaign Train: Zulum Storms Mafa, Dikwa, Gamboru Ngala to Rousing Reception
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce taron, wanda aka gudanar a yau a Damaturu, ya samu halartar dimbin magoya baya da masu goyon bayan gwamnatin Tinubu, waɗanda suka fito domin bayyana matsayarsu kan ci gaba da mulkin shugaban ƙasar, tare da nuna goyon baya ga manufofinsa da shirye-shiryen gwamnatinsa.
Gangamin na Damaturu, wanda Kodinetan Ƙasa na TMGA 2027, Farfesa Sheriff Almuhajir, ya jagoranta a matsayin wanda ya shirya kuma ya kira taron, na zuwa ne a matsayin ci gaba da faɗaɗa ayyukan ƙungiyar a yankin Arewa maso Gabas.
Taron ya samu wakilcin gwamnatin jihar Yobe, inda Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Mohammed Goje ya wakilci gwamnatin, tare da wakilan shugabancin jam’iyyar APC na jihar da sauran manyan masu ruwa da tsaki.
Wakilan sun haɗu da sauran mahalarta wajen bayyana goyon baya da jaddada biyayya ga Shugaba Tinubu da kuma nuna aniyarsu ta ci gaba da kasancewa cikin shirin gangamin TMGA 2027.
Read also: GOV. LAWAL PLEDGES MORE PROJECTS AS APC CAMPAIGN STORMS SHINKAFI LGA
Wannan na zuwa ne bayan babban taron da ƙungiyar ta gudanar a Yola, jihar Adamawa, wanda ya haɗa wakilai daga jihohi shida na yankin.
Gangamin na daga cikin shirin ƙungiyar na gina babbar hanyar haɗa magoya bayan shugaban ƙasa a faɗin Najeriya, tare da faɗaɗa tattaunawa da wayar da kan al’umma game da manufofin gwamnatin tarayya a fannoni daban-daban.
Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da irin waɗannan taruka a sauran jihohin ƙasar nan, domin haɗa matasa, mata, ƙwararru, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki a ƙarƙashin manufar ci gaba, zaman lafiya da wadata.
Almuhajir ya bayyana cewa burin gangamin shi ne tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a matakin jihohi, ƙananan hukumomi da mazabu, tare da tabbatar da cewa saƙon TMGA 2027 ya isa ga jama’a a faɗin ƙasar nan.
Ya kuma yi godiya ga Gwamnatin Jihar Yobe da Shugabancin Jam’iyyar APC na jihar bisa tsayuwa kai da fata dan tabbatar da nasarar gangamin.
Taron na Damaturu ya ƙara nuna yadda gangamin TMGA 2027 ke faɗaɗa ayyukansa a Arewa maso Gabas, yayin da shirin neman goyon bayan jama’a gabanin zaɓen 2027 ke ci gaba da ɗaukar sabon salo.






