Zaben gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027 na daga cikin muhimman zabukan da za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara makoma mai ma’ana ga jihar a fannoni daban- daban na rayuwa.Ba batun sauya fuska ko ci gaba da rike wadanda aka saba gani ba ne kawai a fagen mulki da siyasa. Abu ne da ya shafi gano jagoran da ya fi dacewa wajen karfafa nasarorin da aka samu, tunkarar sabbin kalubale da kuma sanya Gombe a kan turbar samun karin ci gaba mai dorewa.
Ga duk wani dan Gombe mai kishin ci gaba, bai kamata ya auna shugabanci da da son rai ko hayaniyar siyasa ba. Abin da ya kamata a duba shi ne halayya, kwarewa, cancanta iya jagoranci da kuma jajircewa wajen yi wa al’umma hidima.
Read also: There Is Wisdom in Silence: A Lesson from the Political Conduct of Dr. Jamil Isyaku Gwamna
A yau, ba’ a gobe ba Jihar Gombe na bukatar gwamnan da yake da kuzarin aiki tukuru, hangen nesa, da kwarewar tafiyar da manyan hukumomi, hikimar hada kan jama’a masu ra’ayi daban-daban da kuma jarumtar daukar matakan da suka dace, don ci gaban al’umma.
Gombe na bukatar shugaba da zai dauki matasa a matsayin abokan ci gaba, ba ‘yan bangar siyasa ba, mata a matsayin ginshikan bunkasar tattalin arziki ba ’yan kallo ba, sannan al’umma a matsayin masu ruwa da tsaki a harkokin gwamnati ba kawai ‘yan amshin shata ba.
Wadannan siffofi na sama dana zayyana na daga cikin muhimman siffofin da suka ci gaba da bayyana da kuma yin tasiri a tafarkin rayuwa da shugabancin Dr. Jamil Isyaku Gwamna.
A tsawon rayuwarsa ta aiki da mu’amalarsa da jama’a, Dr. Jamil Gwamna ya sha nuna cewa shugabanci hidima ne ga al’umma. Nasarorin da ya samu a bangaren kamfanoni masu zaman kansu daya jagoranta da kuma kokarinsa na samar da damarmaki na ayyukanyi ga matasa da kuma zuba jarinsa a fannin ilimi da kiwon lafiya, da kuma goyon bayansa ga ci gaban matasa, duk suna nuna falsafar iya shugabancinsa cikin salo na mutunci da mutuntawa.
Saboda haka, ba abin mamaki ba ne yadda ya sha bayyana cewa gina dan Adam zai kasance ginshikin gwamnatinsa idan aka ba shi damar yi wa jihar Gombe hidima a matsayin Gwamna.
Read also: THOUGHTS Why Dikko Radda Deserves Second Term
Gina hanyoyi, gadoji da gine-ginen gwamnati abubuwa ne masu muhimmanci, amma ilimantar da ’yan kasa, horar da ma’aikata, samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya, tallafa wa ’yan kasuwa masu kirkire-kirkire da bunkasa matasa Maza da Mata, su ne abubuwan da ke tabbatar da dorewar ci gaban tattalin arziki. Gwamnatin da ta zuba jari a cikin jama’arta, ta zuba jari ne a makomarta.
Haka kuma, Dr. Jamil Gwamna ya fahimci cewa ci gaba mai dorewa yana bukatar ci gaba da kyawawan manufofin da aka gada, tare da kawo sabbin dabaru a inda ake bukata. Jihar Gombe ta samu nasarori masu tarin yawa a karkashin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, musamman a fannonin gine-gine, noma, kiwon lafiya da gyaran harkokin gwamnati da kuma gina dan Adam. A don haka zaben 2027 ya kamata ya dogara ne kan wanda ya shirya tsaf don yin shugabanci bisa adalci da kuma mutunta wayanda zai shugabanta.
Babu tantama ko shakku, takarar Dr. Jamil Isyaku Gwamna ta wuce siyasa kawai. Tana wakiltar kudurin samar da shugabanci nagari, bunkasa jarin dan Adam da kuma gina ci gaba mai dorewa.
Ibrahim Sani Shawai
Mai magana da yawun Dr. Jamil Isyaku Gwamna,
Dan takarar Gwamnan Jihar Gombe na Jam’iyyar APC.

