Yayin da yakin neman zaben shekarar 2027 ke kara daukar zafi a sassa daban-daban na kasar nan, jam’iyyar APC a jihar Gombe ta bullo da wani sabon salo na yakin neman zabe mai daukar hankali. A karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, yakin neman zaben yana hade da kaddamarwa da kuma bude sabbin ayyukan more rayuwa da ke da nufin inganta rayuwar al’umma. Wannan ya sanya yakin neman zaben ya wuce tarukan siyasa da jawabai, Izuwa ga nuna ayyuka da nasarorin da ake samu a kasa.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Ibrahim Sani Shawai Mai Magana da yawun Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya baiwa manema labarai.
Read also: Gov. Abba K. Yusuf set to flag-off 2027 campaign sunday in Rogo
Ya ce abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, da dan takarar gwamnan jam’iyyar ta APC Dr. Jamil Isyaku Gwamna (Sardaunan Gombe), tare da manyan jagorori da masu ruwa da tsaki na APC, ke hada karfi da karfe wajen gudanar da wannan tafiya.
Read also: The 2027 election will be fought for with all strength – Babba Kaita
A yayin da ake karfafa gwiwar magoya baya da wayar da kan al’umma kan manufofin jam’iyyar, ana kuma amfani da damar wajen kaddamar da sabbin ayyuka, bude wadanda aka kammala da nuna irin ci gaban da gwamnatin ke kokarin samarwa a fadin jihar.
Wannan tsari ya kara nuna cewa APC a Gombe ba ta mayar da hankali kan neman kuri’u kawai ba, har ma tana kokarin hada siyasa da ayyukan da jama’a za su iya gani da kuma amfana da su. Yayin da Dr. Jamil Gwamna ke gabatar da manufofinsa na makomar jihar, ana kuma amfani da nasarorin da aka samu a karkashin gwamnatin Inuwa Yahaya a matsayin ginshikin tattaunawa kan ci gaba da fadada ayyukan raya kasa, samar da damarmakin tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
A tsawon kwanaki uku da fara wannan kamfen, an kaddamar da sabuwar Sakatariyar Mulki ta Karamar hukumar Balanga ta kudu. An dasa harsashin ginin hanyar Dalawaja- Walalungada, wacce za ta hada Jihoshin Gombe da iyakar Adamawa. An kaddamar da fara hanyar Talasse- Bangu zuwa boka. An kaddamar da fara hanyar Degri- Sikam. Bugu da Kari an dasa harsashin ginin hanyar Yelwa- Baguji a yankin Dadiya.
A ina za a ga irin wannan salo idan ba a jihar Gombe ba? Dan Majen Gombe Ka San hanya. Ko Gezau an buga da Kai an barka.





