Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Zaben Gwamna A Gombe: Dalilan da Ya Sa Sardaunan Gombe Ya Zama Mafi Sauƙin Ɗan Takarar Gwamna da Za a Gabatar wa Jama’a
    Opinion

    Zaben Gwamna A Gombe: Dalilan da Ya Sa Sardaunan Gombe Ya Zama Mafi Sauƙin Ɗan Takarar Gwamna da Za a Gabatar wa Jama’a

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 19, 20264 Mins Read
    FB IMG 1787177129983
    FB IMG 1787177129983

    Ibrahim Sani shawai

    Yayin da tattaunawar neman gwamnan Jihar Gombe ta 2027 ke ƙara karatowa da kuma kara ɗaukar hankali, masu neman takara za su gabatar da alkawura da manufofi, jawabai, taken Yaƙin Neman Zaɓe da kuma kalaman nuna ƙauna ga jihar Gombe. Amma bayan duk waɗannan alkawura, masu zaɓe suna da damar yin wata muhimmiyar tambaya:

    Me ka yi da damar da aka ba ka a baya, kafin ka nemi mu ba ka wata dama mafi girma?

    A wajen Jamil Isyaku Gwamna, akwai tarihin ayyukan da za a iya dubawa da tantancewa.

    Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi bayyana a tafiyar rayuwarsa ta aikin gwamnati, shugabancin kamfanoni da kuma harkokin kasuwanci shi ne mayar da hankali wajen tallafa wa mutane, musamman al’ummar Jihar Gombe a duk lokacin daya samu dama.

    A lokacin da yake aiki a Hukumar Ruwa ta Jihar Gombe, kafin ya koma bangaren kamfanoni, ya samar da aikin yi ga fiye da mutane 1,000 a lokacin jagorancin sa. A wajen mutane da yawa daga cikin waɗanda suka samu wannan damar, aikin bai tsaya ga samun albashi kawai ba; ya zama hanyar ciyar da iyalai, da tallafa wa ‘yan’uwa da kuma samar da wata dama ta ci gaba a rayuwarsu.

    A Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Kano wato (KEDCO), inda ya kai matsayin babban shugaba, an tabbatar da cewa kimanin matasa 1,500 aka dauka aiki a lokacin jagorancin sa.

    Haka kuma, a Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (KAEDCO), an kiyasta cewa wasu mutane 200 sun samu aikin yi da aka samar a ƙarƙashin jagoranci da tasirinsa.

    Akwai wani muhimmin saƙon siyasa da za a iya fahimta daga wannan: Duk lokacin da Jamil Gwamna ya samu wata dama, sai ya bude hanyoyin taimakawa domin wasu ma su amfana.

    Gudunmawar da Dokta Jamil Gwamna ya bayar bai tsaya ga samar da ayyukan yi kadai ba. Harkar limi ma ya kasance wani muhimmin ɓangare na tallafinsa ga matasan Jihar Gombe.

    A shekara ta 2017 Sardaunan Gombe Ya ɗauki nauyin matasa 39 daga Jihar Gombe domin yin karatu a Yamusa Science College da ke Birnin Kebbi na Jihar Kebbi.

    Har ila yau a shekarar 2019, ya kara ɗaukar nauyin matasa goma ’yan asalin Gombe zuwa ƙasar Morocco domin ci gaba da karatu da samun digiri na farko, abin da ya ba su damar samun ilimi da ƙwarewa tare da faɗaɗa tunaninsu ta hanyar hulɗa da tsarin ilimi na ƙasashen duniya.

    A tsawon shekaru, matasa maza da mata sun kuma amfana daga shirye-shiryen tallafi da suka haɗa da injunan niƙa da markade, da kekunan ɗinki, da firij-firij da sauran kayan aikin da za su taimaka wajen fara ƙananan sana’o’i da bunƙasa hanyoyin samun kuɗin shiga na iyalai.

    Kazalika, tsakanin shekarun 2011 zuwa 2018, kimanin matasa 200 daga Gombe sun amfana da shirin ƙarfafa matasa da ya shafi koyar da sana’o’in gyaran bututun ruwa (plumbing), da walda da kafinta, duk da nufin taimaka musu su samu sana’o’in dogaro da kai da gina ingantacciyar rayuwa.

    Waɗannan abubuwa na iya kasancewa ayyuka daban-daban, amma idan aka duba su gaba ɗaya, suna nuna irin alaƙar da Jamil Gwamna ya daɗe yana da ita da Gombe da al’ummarta—alaƙar da ba don neman kujerar gwamna ta 2027 ta fara ba.

    Shi ya sa ake cewa Jamil Gwamna ɗan takara ne mai sauƙin gabatarwa ga jama’a.

    Yayin da shekarar 2027 ke ƙara matsowa, al’ummar Jihar Gombe na ƙara duba irin ɗan takarar da za su iya auna jajircewarsa da abin da ya riga ya yi fiye da shekaru 20 na tarihin ayyuka da hulɗa da jama’a, maimakon wanda hujjarsa ta fi dogara ne kan alkawura da jawabai da ake yi a kafafen sada zumunta.

    Fiye da shekaru ashirin, Sardaunan Gombe, Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya gina kyakkyawar alaƙa da jama’a, ya tallafa wa mutane, ya samar da damammaki, tare da ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa a sassa daban-daban na jihar.

    Ƙwarewar Dokta Jamil Gwamna ta shafi aikin gwamnati da kuma harkokin kamfanoni masu zaman kansu, abin da ya ba shi damar fahimtar yadda gwamnati ke tafiya a gefe guda, da kuma yadda ake gudanar da shugabanci da harkokin kamfanoni a ɗaya gefen.

    A takaice, tarihin rayuwarsa da ayyukansa ya ba masu zaɓe damar kallon abin da ya riga ya yi, ba wai kawai abin da yake alkawarin zai yi ba. Wannan na daga cikin dalilan daya da al’umma Jihar Gombe ke kiransa da sunan *Jamilu Na Kowa*

    Ibrahim Sani Shawai

    Mai Taimakawa Dokta J

    amil Gwamna a Harkokin Yada Labarai.

    cancantar gombe gwamna jamil jihar
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleIGP DISU ATTENDS NORTH-WEST SECURITY SUMMIT, CALLS FOR COORDINATED REGIONAL RESPONSE TO INSECURITY
    Next Article TINUBU TASKS HOMELAND SECURITY ADVISER TO COORDINATE FIVE-YEAR NATIONAL SECURITY THREAT ASSESSMENT, DEFENCE PLAN

    Related Posts

    Opinion

    Jamil Gwamna: A True Technocrat and the KEDCO Transformation Story — Part 1

    August 17, 2026
    Opinion

    Kano Projects Not Urban-Based: Why Gov Abba Beats All

    August 17, 2026
    Opinion

    2027: Pantami Is No Match for Sardauna’s Integrity in Gombe Politics.

    August 15, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026285 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026158 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026154 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.