Gwamnatin Tarayya ta sake tabbatar da cewa za a kammala tare da ƙaddamar da sashen Kano–Daura–Katsina na aikin layin dogo na Kano–Maradi, mai tsawon kilomita 284, a watan Disamba 2026.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne bayan wani Ayarin hadin gwiwa daga Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Ma’aikatar Kuɗi da kuma masu ba da kuɗin aikin yayin ziyarar duba aikin daga ranar Talata 25 zuwa Alhamis 27 ga Agusta 2026.
Ayarin sun nuna cewa aikin sashen Kano–Katsina ya kai sama da kashi 75 cikin 100, yayin da aka kuma gudanar da gwajin tafiyar jirgin ƙasa a kan layin da aka kammala, inda jami’an suka yi tafiya daga Kazaure zuwa Katsina.
Daraktar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Injiniya Habiba Buhari, wadda ta wakilci Babban Sakataren Ma’aikatar, Injiniya Funso Adebiyi, ta ce aikin yana kan hanyar kammaluwa tare da ƙaddamar dashi a watan Disamba 2026.
Ta ce duk da cewa damina ta ɗan rage saurin aikin, an samu gagarumin ci gaba, musamman ganin cewa an riga an tanadi kayayyakin da ake buƙata domin ci gaba da shimfiɗa layin dogon.
Sai dai ta bayyana cewa aikin na fuskantar wasu ƙalubale da suka haɗa da matsalolin tsaro, satar kayayyakin gini, matsalolin mallakar filaye da hanyar jirgi ta ratsa a wasu birane, haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a kan hanyar Kano–Dutse, da kuma raguwar ayyukan gine-gine a lokacin damina.
Dangane da matsalolin filaye, Injiniya Buhari ta ce gwamnati na tattaunawa da al’ummomin da abin ya shafa domin warware matsalolin tare da tabbatar da cewa ’yan kwangila sun samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ta kuma ce ana ci gaba da shirye-shiryen samar da jiragen ƙasan da za su fara aiki domin tabbatar da cewa an samu kayan aikin da ake buƙata kafin lokacin ƙaddamar da aikin.
Shi ma wakilin masu ba da kuɗin aikin, Siya Biniza, ya bayyana cewa jarin da aka zuba a aikin ya dace, yana mai cewa layin dogo muhimmin ababen more rayuwa ne da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
A nasa ɓangaren, wakilin Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, Alhaji Muhammadu Kamal, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da kashi 15 cikin 100 na kuɗin haɗin gwiwar da ya rataya a kanta.
Ya ce sauran kashi 85 cikin 100 na kuɗin aikin ana samar da shi ne ta hanyar tsarin tallafin kuɗi na rance.
Kamfanin da ke aikin, Mota-Engil Nigeria, ya kuma tabbatar da aniyarsa ta kammala sashen Kano–Katsina zuwa Disamba 2026.
Babban Jami’in Kuɗi na kamfanin, Vladislav Bystrenko, ya ce mataki na farko na aikin, wanda ya haɗa da hanyar Kano–Katsina, zai kammalu a Disamba 2026, yayin da ake sa ran kammala sashen Katsina zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar zuwa ƙarshen shekarar 2027.


