Gwamnatin Tarayya ta amince da ware Naira tiriliyan 1.5 domin sake ginawa da kuma mayar da hanyar Lambata–Bida–Mokwa–Makera–Kontagora ta zama mai layuka biyu, a jihar Neja. Gwamnatin jihar Neja ce ta bayyana hakan, inda ta ce aikin na daga cikin manyan ayyukan inganta hanyoyi da sufuri a jihar.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Hanyar da aikin ya shafa na da muhimmiyar rawa wajen hada manyan garuruwa da al’ummomi a jihar Neja, tare da samar da hanyar zirga-zirga tsakanin jihar da sauran sassan Najeriya. Ana sa ran aikin zai sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci da tattalin arziki a yankunan da hanyar ta ratsa.
Read also: Babban Labari,Gwamnatin Tarayya za ta rage farashin fetur a gidajen NNPCL na wata guda
Read also: Bankin Duniya Ya Ƙara Hasashen Ci gaban Tattalin Arzikin Najeriya zuwa Kashi 4.
Read also: Governor Radda Makes Fresh Appointments, Tasks Appointees on Building Your Future Agenda
Rahoton ya ce an shirya gudanar da bikin aza harsashin ginin aikin a Bida ranar Talata, 13 ga Oktoba 2026, da ƙarfe 12 na rana. Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ne zai jagoranci bikin, yayin da ake sa ran wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa za su halarta.
Daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci bikin akwai Ministan Ayyuka, David Umahi, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, da Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da kuma shugaban kamfanin Hi-Tech Construction. Gwamnatin jihar ta ce aikin zai taimaka wajen inganta hanyoyin tarayya da kuma ƙara haɗin kai tsakanin al’ummomin jihar Neja da sauran sassan ƙasar.

