Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » TARON KADUNA: YAR MANUNIYA TA BAYYANA MATSAYAR ALUMMAR AREWA AKAN SHUGABA TINUBU
    Opinion

    TARON KADUNA: YAR MANUNIYA TA BAYYANA MATSAYAR ALUMMAR AREWA AKAN SHUGABA TINUBU

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanOctober 26, 20268 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1792926403134

    Daga Abdulaziz Abdulaziz

    FB IMG
    FB IMG 1792959208975

    Taron da aka Yi ranar Asabar da ta wuce,a garin Kaduna, tsohuwar cibiyar siyasar Arewa, Arewa ta yi ta ƙara fito da matsayin ta a matsayin ginshiƙin siyasar Najeriya. Wannan babban taro zai ci gaba da damun waɗanda su ka shafe watanni su na yaɗa ƙaryar cewa Arewa ta yi watsi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    Read also: KADUNA RALLY AS THE NORTH’S REFERENDUM ON Tinubu

    Filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna ya cika maƙil, har al’umma su ka bazu zuwa titunan da aka ƙawata da bilbod da tutocin jam’iyyar APC da hotunan shugaban ƙasa. Ko ina ka duba allunan rubutu masu ɗauke da saƙon Arewa for Asiwaju, Sai Tinubu, Tinubu 2 times da sauran su.

    Wannan taro ya kasance wani dandali haɗuwa ne na mutanen Arewa kama daga Hausawa zuwa Fulani, yan Tibi, Idoma, Gbagyi, Yarbanwa, Nupawa, da Barebari. Gwamnonin APC na Arewa gaba ɗaya, tare da goyon bayan takwarorin su na Kudu, sun zauna kafaɗa da kafaɗa da tsofaffin gwamnoni, ƴan majalisu, limamai, fastoci, shugabannin mata da masu sana’o’i waɗanda su ka taka kilomita da dama domin ganin mutumin da har yanzu suke kira Jagaba, wato jagora.

    Wannan taro ya wuce taron al’ummar da aka biya kuɗi domin su halarta, taro ne na gaske, mai cike da ɗimbin al’umma, kuma mai cike da shauƙi. Wasu hotuna daga taron sun bayyana hakan sosai, ka duba hoton wasu mutane uku masu cike da farin ciki su na ɗagawa shugaban ƙasar su hannu, yayin da shi kuma ya sauke gilashin motar sa domin gaishe su. Dubi hotunan ɗimbin mutanen da su ka kwana a wurin taron domin su samu gurbi mai kyau na shaida abin tarihi, da kuma hotunan matasa maza da mata masu murna waɗanda su ka shafe yini guda a cikin rana su na kaɗa tutoci tare da rera yabon shugaban.

    Wannan saƙon Arewa ne, saƙo ne da yake cewa har yanzu Arewa na tare da mai ƙaunarta.

    Kamar yadda na rubuta a watan Fabrairun 2023, a lokacin yaƙin neman zaɓe na baya, lokacin da wasu mutane su ka yi ƙoƙarin tunzura mutane saboda ƙabilanci domin su juya ra’ayin al’umma a kan sa, Asiwaju Tinubu da Arewa sun daɗe su na abota. Wannan abota ba ta neman cin moriya ba ce kawai. Abota ce mai tushe a tarihi. Wasu da dama basu sani ba cewa tafiyar siyasar Tinubu ba ta fara a Legas ba. Ta fara ne da Arewa.

    A shekarar 1991, a farkon Jamhuriya ta Uku wadda ba ta samu nasarar kammaluwa ba, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya kafa jam’iyyun siyasa guda biyu, Tinubu yana da zaɓin yin siyasa da ƴan uwansa Yarabawa. Shaharraren ɗan siyasar Legas, Cif Lateef Jakande, yana cikin harkar siyasa. Duk da haka, Tinubu ya zaɓi ya haɗa kai da ƙungiyar siyasa ta Peoples Front (PF) ta Janar Shehu Musa Yar’Adua.

    A ƙarƙashin jam’iyyar SDP, ta hanyar wannan ƙungiya ta PF, Tinubu ya zama Sanatan Legas ta Yamma a shekarar 1992. Lokacin da MKO Abiola ya zama ɗan takarar SDP, Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin matsa lamba domin Ambasada Babagana Kingibe, ɗan asalin Borno, ya zama abokin takarar Abiola a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

    Wannan zaɓin da ya yi a shekarar 1991 shi ne ya tsara salon siyasar sa tun daga lokacin har zuwa yau.

    Lokacin da Shugaba Obasanjo ya so murƙushe Atiku Abubakar a shekarar 2007, Bola Tinubu ne ya zama mai ceton sa. A shekarar 2011, ya taimakawa Nuhu Ribadu domin ya yi takarar shugaban ƙasw, sannan ya taimakawa Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 da na 2019. Haka nan a shekarar 2011, ya goyi bayan Aminu Tambuwal domin zama Kakakin Majalisar Wakilai, a lokacin da jam’iyyar sa ta PDP ta yi adawa da shi.

    Babu wani ɗan siyasar Kudu da ya zuba jarin siyasa mai yawa irin wannan domin tallafawa Arewa.

    Haƙiƙa, Arewa ba ta mantawa da halarci.

    Wannan ne ya sa ƙungiyar Arewa for Asiwaju, wata ƙungiyar siyasa da ta ƙunshi manyan jiga-jigan siyasar Arewa, ta cancanci yabo saboda wannan mataki da ta ɗauka a daidai lokacin da ya dace.

    A lokacin da ƴan adawa ba su da abin da za su gabatar sai tsoffin batutuwan tallafin man fetur da aka cire, waɗanda a ke iƙirarin cewa ba su dace da dokar PIA ba, tare da ƙaryace-ƙaryacen da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI, waɗanda Gwamna Uba Sani ya yi gargaɗi a kan su yadda ya kamata a Kaduna, A4A tana samar da abin da Arewa ta fi buƙata, wato tattaunawa ta gaskiya cikin Hausa, Fulfulde, Tiv, Nupe, Gbagyi da Kanuri, a kowace kasuwa, tashar mota, masallaci da coci.

    A4A ba wai ƙungiya ce ta yaƙin neman zaɓe ba kawai. Tunatarwa ce cewa abota tana buƙatar amana daga ɓangarori biyu, kuma Arewa tana da riƙo da aƙidunta ta na adalci, gaskiya, zaman lafiya da jituwa, da kuma haɗin kan ƙasa.

    A matsayin ta na ƙungiyar siyasa, babban manufar A4A ita ce samar da haɗin kan al’ummarmu da gudanar da yaƙin neman zaɓe bisa hujjoji. Manufar ita ce a mayar da martani ga ƙaryar cewa Shugaba Asiwaju Tinubu ya yi watsi da abokansa mutanen Arewa tun bayan da ya zama shugaban ƙasa.

    Ta yaya? Shin ta hanyar kafa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo, wadda Arewa ta daɗe tana buƙata tsawon shekaru 60? Ko ta hanyar kafa Hukumar Bunƙasa Arewa ta Tsakiya da Hukumar Bunƙasa Arewa maso Yamma? Ko ta hanyar sabbin jami’o’in tarayya a Mubi, Kachia da Kabo?

    Shin mutumin da ya yi watsi da Arewa zai yi gaggawar kammala layin dogo na Kano zuwa Maradi ko kuma hanyar Akwanga–Lafia–Makurdi? Shin zai kafa cibiyoyin kula da cutar daji (cancer) tare da inganta asibitoci da makarantu da dama?

    Read also: Kano Steals the Show in Kaduna: Abba Yusuf Emerges as Tinubu’s Political Mobiliser

    Arewa for Asiwaju tana gabatar da waɗannan tambayoyi ne tare da hujjoji masu ƙarfi.

    Kaduna ta samar da wata dama ta ƙara rusa hayaniyar ƴan adawa marar tushe. Arewa ta haɗu ta fito da murya ɗaya mai ƙarfi. Gwamnoni 18 daga cikin 19, jerin tsofaffin gwamnoni tun daga waɗanda su ka fara mulki a 1999 zuwa yau, ɗimbin matasan ƴan siyasa masu tasowa, da rundunar masoya jam’iyya, duk sun halarta.

    Abun abin sha’awa ne.

    Tsawon watanni, wasu ƴan tsirarun mutane amma masu yawan surutu a Abuja da shafukan sada zumunta sun yi ta ƙoƙarin yaɗa wani labari na ƙarya cewa Arewa ta yi nadamar zaɓen Tinubu a 2023, cewa shugaban ƙasa da masu yaƙin neman zaɓen sa ba za su iya sake shiga Arewa ba, kuma an riga an yanke hukuncin zaɓen 2027 tun yanzu.

    Taro ɗaya a Kaduna ya binne wannan ƙaryar.

    Kamar yadda Darakta Janar na Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana duk wani muhimmin mutum a Arewa yana filin wasan jiya. Yawancin su sun halarta da kan su, yayin da wasu da dama su ke tare da su a zuciya. Ƙalilan masu adawa waɗanda su ka watse ba su da wani tasiri da zai iya haifar da babban sauyi a siyasa.

    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Yari ba su zo Kaduna domin yin dogon jawabi mai cike da kalmomin siyasa ba kawai. Sun zo da tarihi da kuma hujjojin da za su tabbatar da maganganun su.

    Kamar yadda aka saba, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya yi magana kai tsaye kuma cikin kaifin basira. Ya yi amfani da saƙo mai ƙarfi domin tunatar da masu zaɓe a Arewa zaɓuɓɓukan da su ke da su.

    Ya ce, “Ba don mun fi kowa hikima ko arziƙi muka yi nasara a shekarar 2023 ba, sai don kun duba zaɓuɓɓukan da ke gaban ku, ku ka fahimci cewa ɗaya zaɓin zai jefa ƙasa cikin masifa. Mun zo ne domin mu roƙe ku ku sabunta wa APC wa’adin mulki na biyu, daga sama har ƙasa.”

    Sanata Yari, wanda ya bayyana farin cikinsa a fili ya tabbatar da cewa: “Da yardar Allah, Arewacin Najeriya tana goyon bayan ka, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, 100 bisa 100, kuma mun ƙuduri aniyar cika alƙawarin mu a ranar 16 ga watan Janairu, 2027.

    Ya kuma ƙara da cewa ya kamata Shugaba Tinubu ya kwanta ya huta, ya jira nasara.

    Wani abin sha’awa shi ne Shugaba Tinubu bai je Kaduna domin neman ƙuri’u ko nuna yawan magoya bayan sa ba kawai. Ya je ne tare da ayyukan da aka aiwatar.

    A wani abu da ba a saba gani ba a tarukan yaƙin neman zaɓe, Shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan dama wurin ƙaddamar da ɓangaren hanyar Kaduna zuwa Abuja mai tsawon kilomita 81, ta hanyar yanka ƙyalle a matsayin alamar ƙaddamarwa.

    Wannan ɗaya ne kawai daga cikin ɗimbin alherin da Kaduna ta samu daga gwamnatin Tinubu. A jawabin sa na maraba, Gwamna Uba Sani ya lissafa fa’idoji da dama da jihar Kaduna ta samu daga gwamnatin Tinubu, waɗanda su ka haɗa da hanyoyi, layin dogo, jami’o’i da cibiyoyin kiwon lafiya.

    Kamar yadda Gwamna Sani ya tabbatar, Arewa ba ta taɓa samun irin wannan alheri ba a baya.

    Shugaba Tinubu yana mayar da martani ga amincin da aka nuna masa ta hanyar ayyukan raya ƙasa, gine-gine masu ɗorewa da kulawa da al’umma.

    Daga Peoples Front a shekarar 1991 zuwa Arewa for Asiwaju a shekarar 2026, Shugaba Tinubu ya kasance yana tafiyar da siyasa a matsayin aboki na gaskiya.

    Read also: Sardaunan Gombe: Hasken Rana Leka Gidan Kowa: Jamil Gwamna, Jagoran Da Yake Da Burin Cigaba Da Gina Jihar Gombe

    Kaduna ta tabbatar da hakan a jiya. A ranar 16 ga watan Janairu, 2027, akwatin zaɓe zai tabbatar da hakan da murya mafi ƙarfi.

    Abdulaziz Abdulaziz shi ne Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan HarkokinYaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, kuma Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Arewa for Asiwaju.

    FB IMG
    FB IMG 1792954982133
    FB IMG
    FB IMG 1792955457281
    arewa Kaduna Rallye testament
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleJAGA HAILS SPEAKER ABBAS TAJUDEEN AS OVER 3.000 BENEFIT RENEWED HOPE EMPOWERMENT PROGRAMME IN ZARIA FEDERAL CONSTITUENCY.
    Next Article Kano Steals the Show in Kaduna: Abba Yusuf Emerges as Tinubu’s Political Mobiliser

    Related Posts

    Opinion

    Sardaunan Gombe: Hasken Rana Leka Gidan Kowa: Jamil Gwamna, Jagoran Da Yake Da Burin Cigaba Da Gina Jihar Gombe

    October 26, 2026
    Opinion

    Kano Steals the Show in Kaduna: Abba Yusuf Emerges as Tinubu’s Political Mobiliser

    October 26, 2026
    Opinion

    KADUNA RALLY AS THE NORTH’S REFERENDUM ON Tinubu

    October 25, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026385 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026355 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026262 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026253 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026199 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026180 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.