Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»News»Najeriya Na Alfaharin Karɓar Baƙuncin Taron Ƙasa da Ƙasa na Hulɗa da Jama’a – Ministan Yaɗa Labarai
    News

    Najeriya Na Alfaharin Karɓar Baƙuncin Taron Ƙasa da Ƙasa na Hulɗa da Jama’a – Ministan Yaɗa Labarai

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanNovember 18, 20264 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1794998068635

    Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa karɓar baƙuncin taron ƙasa da ƙasa na hulɗa da jama’a na shekarar 2026 (World Public Relations Forum, WPRF) da Nijeriya ta yi yana nuna yadda ƙasashen duniya ke ƙara amincewa da ita, da bunƙasar ƙwarewar ma’aikatan ta da kuma gudummawar ta ga harkokin sadarwa a duniya.

    Da yake jawabi a wajen buɗe taron a Abuja, ministan ya ce Nijeriya na alfahari da kasancewa ƙasa ta farko a Yammacin Afirka, kuma ta biyu a nahiyar Afirka da ta karɓi baƙuncin wannan gagarumin taro na duniya.

    Read also: EXECUTIVE COUNCIL MEETING,ENGR JAGA CHAIRS 19 COUNCIL MEETING,FLAGS OFF NPC E-REGISTRATION IN ZARIA.

    Idris ya ce: “Zaɓen Nijeriya a matsayin mai masaukin baƙuncin taron ƙasa da ƙasa na hulɗa da jama’a na shekarar 2026, ya nuna cewa ƙungiyar ƙwararrun harkokin hulɗa da jama’a ta duniya ta amince da ƙarin ɗaukakar da ƙasar mu take samu a duniya, ƙwarewar da muke da ita da kuma gudunmawar mu ga harkokin sadarwa a duniya. Muna alfahari da tarbar wakilai daga sassa daban-daban na duniya domin nuna musu irin abubuwan da Nijeriya take da su.”

    Ministan, wanda ya tarbi mahalarta taron a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gode wa Farfesa Justin Green, Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa ta Hulɗa da Jama’a da Gudanar da Sadarwa (Global Alliance for Public Relations and Communication Management), tare da tawagar sa, bisa amincewa da Nijeriya.

    Haka kuma ya yaba wa Shugaban Cibiyar Ƙwararrun Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku, da tawagar sa, bisa ƙoƙarin da suka yi na ganin Nijeriya ta samu damar karɓar baƙuncin taron da shirya shi.

    Ya ce taken taron na bana, wato “Sadarwa Mai Inganci da Ɗaukar Nauyi: Muryar Jama’ar Duniya”, ya zo a daidai lokacin da harkokin sadarwa suke fuskantar ƙalubale sakamakon bunƙasar basirar na’ura mai ƙwaƙwalwa (AI), yaɗa bayanan ƙarya, yaɗa bayanan da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a da kuma amfani da fasahar zamani wajen murɗe bayanai.

    Read also: SNB KADUNA STATE CHAPTER CONGRATULATES PROF ADAMA ON HER ELEVATION TO PROFESSOR.

    Ya ce: “Dimokiraɗiyya na bunƙasa ne idan ’yan ƙasa suna da ’yancin bayyana ra’ayoyin su, tambayar masu mulki, samun bayanai da kuma shiga tattaunawar da ta shafi ƙasa. Mun yi imani da cewa dole ne kafafen yaɗa labarai su kasance masu ’yanci domin gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora musu, tare da kiyaye sahihanci, adalci da ƙa’idojin aikin jarida.

    “Dole ne sadarwa mai ɗauke da nauyi ta kare gaskiya ba tare da tauye haƙƙin mutane na bayyana ra’ayoyin su mabambanta ba.”

    Idris ya lura da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba da tabbacin ’yancin faɗar albarkacin baki, tare da amincewa da rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen bin gwamnati bahasin ayyukan ta.

    Ya yi tsokaci kan goyon bayan da Gwamnatin Tarayya take bayarwa wajen kafa Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta UNESCO mai kula da Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai da Bayanai (IMILI), wadda za ta kasance cibiyar aji na biyu ta UNESCO a Abuja, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ilimin yaɗa labarai da sarrafa bayanai.

    Ministan ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai ɗimbin al’adu, fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire, albarkatun ƙasa da haziƙan mutane. Ya ce waƙoƙi, finafinai, adabi, abinci da kuma ruhin kasuwanci suna daga cikin abubuwan da suka sa ƙasar take samun karɓuwa a idon duniya.

    Read also: Governor Radda Joins Vice President Shettima, Other Dignitaries at Senator Dandutse’s Daughter’s Wedding

    Ya buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da wannan damar wajen gina dangantaka mai ɗorewa, musayar ra’ayoyi da ƙarfafa ƙwarewar sana’ar sadarwa a duniya, tare da sanin al’adu daban-daban da kuma damar da Nijeriya ke da su.

    Taron Ƙasa da Ƙasa na Hulɗa da Jama’a na shekarar 2026 ya haɗa ƙwararru a fannin hulɗa da jama’a da sadarwa daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna rawar da sadarwa mai ɗaukar nauyi za ta taka wajen magance ƙalubalen duniya da kuma ƙarfafa wannan sana’a.

    FB IMG
    FB IMG 1794998076708
    FB IMG
    FB IMG 1794998064693
    FB IMG
    FB IMG 1794998072755
    FB IMG
    FB IMG 1794998060177
    international nigeria public relations summit
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleTinubu ya amince da samar da tashar tsandauri a Jihar Kebbi
    Next Article Kano 2027: Labour Union, Pensioners Endorse Abba Yusuf for Second Term

    Related Posts

    News

    PRESIDENT TINUBU MOURNS FORMER LAGOS DEPUTY GOVERNOR SEN. IDIAT ADEBULE

    November 28, 2026
    News

    Just In: PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU SIGNS FOUR BILLS INTO LAW AS PRESENTED TO HIM BY THE HOUSE OF REPRESENTATIVES.

    November 28, 2026
    News

    S A To Gov. IDRIS’Extends Humanitarian Service, Donates Motorised Borehole To Community In Dakingari.

    November 28, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.