Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»News»Tinubu ya amince da samar da tashar tsandauri a Jihar Kebbi
    News

    Tinubu ya amince da samar da tashar tsandauri a Jihar Kebbi

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanNovember 18, 20262 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1794998121852

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar samar da tashar tsandauri (Inland Dry Port) a Jihar Kebbi, yana mai cewa an amince da aikin domin biyan buƙatar jihar na inganta harkokin kasuwanci da sufuri.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Jihar Kebbi domin neman goyon bayan al’umma a yunƙurinsa na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

    Read also: Tinubu Honours 25 Victims Of NAF 931 Aircraft Accident, Donates Houses, N100m To Each Deceased Family*

    A yayin jawabin nasa, Shugaban Ƙasar ya ce ya karɓi buƙatun da Gwamnan Jihar Kebbi ya gabatar masa, ciki har da samar da tashar tsandauri, tare da wasu ayyukan hanyoyi da gyaran hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata.

    Read also: 2027: After Clerics, Barau Mobilises 3,405 Traditional Rulers in Kano for Tinubu, Abba, Other APC Candidates

    “Na fahimci buƙatarku game da tashar tsandauri. An amince da ita. Kebbi tana buƙatar wannan aiki, kuma an amince da shi,” in ji Shugaban Ƙasar.

    Tinubu ya kuma gode wa al’ummar Kebbi bisa goyon bayan da suka ba shi a zaɓen 2023, inda ya bayyana cewa ya je jihar ne domin nuna godiya da kuma neman goyon bayansu a karo na biyu domin kammala ayyukan da ya fara.

    Read also: NWDC Chairman Denies Blocking Distribution of Vehicles, Equipment, Foodstuffs

    Ya tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da aiki domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da samar da abubuwan more rayuwa.

    Haka kuma, ya buƙaci matasa da sauran al’ummar jihar da su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, tare da yin amfani da katin zaɓensu wajen shiga harkokin dimokuraɗiyya.

    FB IMG
    FB IMG 1794998142907
    FB IMG
    FB IMG 1794998129636
    FB IMG
    FB IMG 1794998116669
    approved dry inland kebbi pbat port
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleNajeriya ta kasance kan gaba a duniya wajen gurfanar da ‘yan ta’adda da yanke musu hukunci – Tinubu
    Next Article Najeriya Na Alfaharin Karɓar Baƙuncin Taron Ƙasa da Ƙasa na Hulɗa da Jama’a – Ministan Yaɗa Labarai

    Related Posts

    News

    INEC ready for Saturday’s mock election in Yobe, declares 158,652 PVCs unclaimed

    November 27, 2026
    News

    Governor Radda Joins Vice President Shettima, Other Dignitaries at Senator Dandutse’s Daughter’s Wedding

    November 27, 2026
    News

    Governor Radda, Kaduna Counterpart Receive Vice President Shettima at Nigerian Air Force Base, Kaduna

    November 27, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026218 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.