Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya tabbatar da cewa al’ummar Borno da sauran jihohin Arewa maso Gabas za su fito ƙwansu da kwarkwatarsu domin zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, yana mai danganta hakan da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a yankin.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Zulum ya bayyana haka ne a wajen gangamin Sabunta Fata na APC a Maiduguri, inda ya yabawa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) bisa tallafin da take bai wa Borno da sauran jihohin yankin, musamman wajen gina hanyoyi, gadoji da sauran muhimman ayyukan more rayuwa. Ya kuma yaba da shirin samar da motocin lantarki guda 10,000 ga yankin, yana mai cewa waɗannan ayyuka na nuna yadda gwamnatin Tinubu ke kawo sauyi a Arewa maso Gabas.
Read also: Governor Radda Assures APC Northwest Reconciliation Committee of Party Unity
Read also: Gov. Abba K. Yusuf set to flag-off 2027 campaign sunday in Rogo
Gwamnan ya kuma roƙi Shugaba Tinubu da ya duba batun dawo da aikin neman man fetur a Kolmani da gaɓar Tafkin Chadi, tare da faɗaɗa layin dogo domin ya haɗa dukkan jihohin Arewa maso Gabas. Ya ce al’ummar yankin za su zaɓi Tinubu da APC a 2027 domin ci gaba da ayyukan da ake gudanarwa da kuma ƙara samun ci gaba.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yabawa Tinubu bisa gina muhimman hanyoyi, kafa sabbin cibiyoyin gwamnatin tarayya, fara aikin Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Gwoza, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da kuma shirin bunƙasa manyan makarantu a Monguno. Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna jajircewa wajen farfaɗo da Arewa maso Gabas, inda ya kuma kalubalanci masu ikirarin bayar da gudunmawa ga yankin da su nuna ayyukan ci gaba masu ɗorewa da suka yi wa talakawa, yana mai jaddada cewa APC na da hujjojin ayyukan da ake gani a ƙasa.




