Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Arewa maso Gabas, tare da umartar jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen fatattakar ’yan ta’addan da ke gudun hijira bayan hare-haren da ake kai musu.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a Maiduguri, Jihar Borno, ranar Laraba, yayin gangamin yaƙin neman zaben APC, inda ya ce zaman lafiyar da aka samu a yankin sakamakon ƙoƙarin sojoji da haɗin kan al’umma za a tabbatar da dorewarsa tare da mayar da shi cikakken farfaɗowar tattalin arziki. Ya kuma yaba wa Gwamna Babagana Zulum bisa dawo da jihar kan turbar ci gaba, inda ya ce ya ƙaddamar da wasu ayyuka da suka haɗa da masaukin mata na NYSC da Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Borno.
Read also: Governor Radda Assures APC Northwest Reconciliation Committee of Party Unity
Read also: MY GOV’T HAS PROJECTS WORTH ₦109 BILLION IN MARU LGA, GOV. LAWAL DECLARES DURING APC CAMPAIGN RALLY
Read also: GOV. LAWAL PLEDGES MORE PROJECTS AS APC CAMPAIGN STORMS SHINKAFI LGA
Shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan ta’adda da su miƙa wuya tare da ajiye makamansu, sannan ya tabbatar wa jami’an tsaro da ke yaƙi da ta’addanci cewa gwamnati za ta ƙara kula da walwala da jin daɗin iyalansu. Ya kuma ce za a ƙara ƙarfafa tattara bayanan sirri domin ceto ɗaliban da aka sace a Askira Uba, yana mai fatan za a kuɓutar da su cikin gaggawa. Tinubu ya danganta nasarorin tsaro da aka samu da haɗin kan shugabanni da al’ummar yankin.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yabawa Tinubu bisa tallafin da yake bai wa Borno da sauran jihohin Arewa maso Gabas, yana mai cewa ya kamata a ba shi damar ci gaba da mulki na wa’adi na biyu. Gwamna Zulum ma ya yaba da ayyukan gwamnatin tarayya, ciki har da jami’o’i, hanyoyi da sauran ababen more rayuwa, musamman hanyar Biu–Maiduguri. Ya kuma yaba wa NEDC bisa samar da motocin lantarki guda 10,000 ga yankin, yayin da shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya miƙa tutocin jam’iyyar ga ’yan takararta a jihar.


