Gwamnatin Tarayya ta bayyana gamsuwarta da ci gaban aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano, inda ta sake tabbatar da shirin ƙaddamar da aikin a watan Disamba.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri, Funso Adebiyi, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar duba aikin da jami’an Ofishin Kula da Basussukan Ƙasa (DMO) da sauran jami’an gwamnati suka gudanar daga Jaji zuwa tashar Kano. Ya ce tashar Kano ta kusa kammaluwa, inda sanya allon sunanta ne kawai ya rage.
Read also: Over 5,000 People Benefits From German Supported Project in Kaduna
Adebiyi ya ce an kammala gyare-gyaren da aka buƙata bayan ziyarar duba aikin da ta gabata, ciki har da maye gurbin gilashin da ke wuraren fasinjoji domin ƙara tsaro, da sauya fitilun tashoshin zuwa waɗanda za su iya aiki na aƙalla shekaru uku. Haka kuma, an samar da na’urorin ɗagawa domin aikin gyara, tare da shirin horas da injiniyoyin Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya kan gudanar da ayyukan tashoshin.
Read also: Kwankwaso Should Stop Dragging Gov. Yusuf into His EFCC Troubles, Kano Government Declares
Ya bayyana cewa ma’aikatar na neman amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin gudanar da gwajin zirga-zirgar jirgin ƙasan na tsawon watanni uku daga Jaji zuwa Kano, wanda zai iya kasancewa kyauta ga fasinjoji.
Ya ce gwajin zai taimaka wajen tantance ingancin layin dogo da tsarin gudanar da zirga-zirga kafin fara jigilar fasinjoji ta kasuwanci. Ya kuma ce gadar da za ta haɗa sauran ɓangaren aikin tsakanin Jaji da Kaduna ta kusa kammaluwa, yayin da ake faɗaɗa tashar Kaduna domin karɓar ƙarin fasinjoji.
A nasa ɓangaren, Daraktar Janar ta DMO, Patience Oniha, ta yaba da ingancin aikin tare da jin daɗin yadda aka gudanar da shi. Adebiyi ya kuma bayyana cewa aikin layin dogo daga Kano zuwa Kazaure, Daura da Katsina na ci gaba, duk da wasu ƙalubalen mallakar filaye. Ya ce layin dogon Kaduna zuwa Kano wani ɓangare ne na babban shirin haɗa manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a Najeriya ta hanyar sufurin jiragen ƙasa.




