Gwamnatin Tarayya, ta hannun Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki (TCN), tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Kano, ta ƙaddamar da tashoshin wutar lantarki guda huɗu da za su ƙara ƙarfin isar da wutar lantarki da megawatt 544. Tashoshin suna Walalambe, Kumbotso, Dakata da Dan-Agundi, kuma ana sa ran za su inganta samar da wutar lantarki ga masana’antu, ’yan kasuwa da mazauna jihar.
A Walalambe, an girka transfoma biyu masu ƙarfin MVA 40 kowannensu, wanda ya samar da ƙarin ƙarfin megawatt 80. Kumbotso kuma ta samu ƙarin transfoma masu ƙarfin MVA 300 a matakin 330kV da kuma transfoma masu ƙarfin MVA 100. Haka kuma, Dakata da Dan-Agundi kowannensu ya samu ƙarin transfoma mai ƙarfin MVA 100 a matakin 132kV. Waɗannan ayyukan za su taimaka wajen rage cunkoson kaya a wasu tashoshi tare da ba da damar samar da wutar lantarki ga buƙatun da a baya ba a iya biya ba.
Read also: Minister, Governor Radda Commission 120MVA Kankia Substation
A Walalambe, an samar da layukan fitar da wuta guda shida da za su taimaka wajen samar da wutar lantarki ga Masana’antar Tokarawa, hanyar Eastern Bypass, titin Maiduguri, titin Hadejia da yankunan da ke kewaye. Kamfanin masana’antu na Lee Group ya koma amfani da wutar lantarkin gwamnati bayan shafe fiye da shekaru 30 yana samar da tasa wutar da kansa.
Read also: Sauye-sauyen Tinubu suna gina Nijeriya mai ƙarfi, Idris ya shaida wa ƙungiyar mata .
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce haka kuma, tashar Dan-Agundi, wadda gobara ta lalata, ta samu damar dawo da wani babban ɓangare na ƙarfinta na samar da wutar lantarki ga cikin birnin Kano, fadar Mai Martaba Sarkin Kano da sauran yankunan da ke kusa.
A cikin wata sanarwa da Adeola Labzy, mai ba wa Ministan wutar lantarki shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, ya sanya wa hannu, ya bayyana ayyukan a matsayin wata shaida ta ƙudurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da ajandar Renewed Hope. Sanarwar ta ce zuba jari a irin waɗannan muhimman ababen more rayuwa zai ƙarfafa masana’antu, ƙananan sana’o’i, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma, tare da mayar da wutar lantarki ginshiƙin bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.

