● Shugaban ƙasar ya gargaɗi ‘yan siyasa da magoya bayansu kan tayar da zaune tsaye, ya ce ba za a lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da dimokuraɗiyya ba.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su ɗauki tsauraran matakai kan masu aikata ta’addancin siyasa da sauran ayyukan da suka saɓa wa tsarin dimokuraɗiyya, yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
Read also: MY GOV’T HAS PROJECTS WORTH ₦109 BILLION IN MARU LGA, GOV. LAWAL DECLARES DURING APC CAMPAIGN RALLY
Shugaban ƙasar ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani nau’in tashin hankali, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma a lokacin yaƙin neman zaɓe ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Juma’a, biyo bayan rahotannin tashe-tashen hankula da suka riƙa faruwa a wasu sassan ƙasar yayin gudanar da harkokin siyasa.
Shugaban ƙasar ya ce duk wani nau’in tashin hankali abin Allah wadai ne, yana mai cewa bai kamata a samu tashin hankali a harkokin yaƙin neman zaɓe ba yayin da ƙasar ke shirin tunkarar zaɓen 2027.
Ya buƙaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su mayar da hankali wajen gabatar da manufofi da ra’ayoyin da za su inganta rayuwar ‘yan Najeriya da bunƙasa ƙasa, maimakon rikice-rikice da gaba da juna.
Read also: Campaign Train: Zulum Storms Mafa, Dikwa, Gamboru Ngala to Rousing Reception
“Ni Jagoran ƙasar nan ne, kuma na ɗaukar wa kaina alhakin tabbatar da zaɓe cikin lumana, ‘yanci da adalci. Ina kira ga shugabannin siyasa da magoya bayansu a dukkan jam’iyyu da su kasance masu ɗa’a da sanin ya kamata,” in ji shugaban ƙasar.
Tinubu ya kuma jaddada cewa bambancin jam’iyya ko burin neman wani matsayi bai kamata ya mayar da ‘yan siyasa abokan gaba ba, domin dukkan ‘yan Najeriya al’umma ɗaya ce.
Ya ƙara da cewa dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suna da ‘yancin gudanar da yakin neman zaɓe a duk inda suke a faɗin ƙasar ba tare da fuskantar barazana, tsangwama ko cin zarafi ba.
Shugaban ƙasar ya ce ya bai wa hukumomin tsaro izinin amfani da cikakken ƙarfinsu wajen fuskantar masu aikata ta’addancin siyasa da sauran ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsarin zaɓe.
Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin hare-hare da tashe-tashen hankula a wasu wuraren gudanar da harkokin siyasa a ƙasar, lamarin da ya ƙara jaddada muhimmancin tabbatar da tsaro da zaman lafiya gabanin babban zaɓen 2027.
Tinubu ya bayyana cewa burin neman mulki ko bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama dalilin zubar da jini ko haddasa rikici ba, yana mai buƙatar dukkan ɓangarori su ba da gudummawa wajen tabbatar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

