Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), a yau Lahadi, ya karɓi baƙuncin bikin ƙaddamar da rabon kayan aikin kashe gobara ga hukumomi da cibiyoyin kashe gobara daban-daban, tare da ƙaddamar da wani babban shirin bayar da kiwon lafiya kyauta ga al’umma. Kakakin Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, PhD, GCON, ne ya samar da waɗannan muhimman ayyuka.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Galadima Ishaq Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙaramar Hukuma (Chief Press Secretary)ya sanyawa hannu,
Read also: Nigeria’s future lies with young population—Speaker Abbas
Sanarwar ta ce kayayyakin aikin kashe gobarar da aka rabawa cibiyoyin sun haɗa da tufafi na musamman masu kariya ga jami’an kashe gobara, wando da rigunan aiki, bututun kai da isar da ruwa, sinadarai na kashe gobara da sauran muhimman kayan aiki. Wannan tallafi zai taimaka wajen inganta ayyukan jami’an kashe gobara da ƙarfafa shirye-shiryensu na tunkarar aukuwar gobara da sauran haɗurra.
Cibiyoyin da suka amfana da wannan tallafi sun haɗa da:
1. Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, reshen Jihar Kaduna.
2. Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, reshen Zaria.
3. Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, reshen Sabon Gari.
4. Sashen Kashe Gobara na Jami’ar Ahmadu Bello, Kongo/Samaru.
5. Sashen Kashe Gobara na Jami’ar Ilimi ta Tarayya.
6. Sashen Kashe Gobara na Kwalejin Koyon Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Najeriya.
7. Sashen Kashe Gobara na Cibiyar Fasahar Sufuri ta Najeriya (NITT).
8. Sashen Kashe Gobara na Kofar Doka.
Read also: EXECUTIVE COUNCIL MEETING,ENGR JAGA CHAIRS 19 COUNCIL MEETING,FLAGS OFF NPC E-REGISTRATION IN ZARIA.
A jawabinsa, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya bayyana irin gudunmawar da gwamnatin Zaria ke bayarwa wajen inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya bayyana cewa, daga cikin irin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen na Karamar Hukumar Zaria karkashin jagorancin shi akwai gina cibiyar Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya a harabar Abdulra’uf Jisambo Complex, Ma’aikatar Ayyuka (Works Department), dake gundumar Kwarbai B cikin Birnin Zaria .
Wannan cibiya za ta ƙara inganta saurin kai ɗauki a lokacin aukuwar gobara da sauran haɗurra, tare da taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a da cibiyoyin da darajarsu ta haura naira biliyan 6.9.
Injiniya Jaga ya nuna matuƙar godiyarsa ga Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, bisa wannan gagarumin yunƙuri da ya samar, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka na da matuƙar muhimmanci wajen kare rayukan jama’a, inganta kiwon lafiya da bunƙasa al’umma. Haka kuma, ya yaba da goyon baya da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani , CON, wajen samar da shirye-shiryen ci gaba da tallafa wa al’umma.
Haka kuma, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya halarci ƙaddamar da shirin bayar da kiwon lafiya kyauta, wanda ake sa ran zai amfanar da sama da mutum 30,000 a faɗin Ƙananan Hukumomin Zaria da Sabon Gari.
Ayyukan da shirin ya ƙunsa sun haɗa da duba marasa lafiya, ba da magunguna da sauran kayan aikin lafiya, gwajin ido da tiyatar majinyatan da ke fama da matsalar ido (Cataract), gwaje-gwajen kunne, hanci da maƙogwaro, bayar da na’urorin taimakon ji ga masu matsalar ji, da kuma tallafin kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai, ciki har da rabon kayan taimakon haihuwa.
An ware cibiyoyi uku domin gudanar da wannan shiri, waɗanda suka haɗa da Asibitin Iya Abdullah da ke Jamawa, Cibiyar Matasa ta Tudun Wada, da Asibitin Saidu Dange da ke Railway, Sabon Gari.
Shugaban ya yi kira ga mazauna yankunan da za su amfana da shirin da su yi amfani da wannan dama wajen samun kulawar lafiya da ake bayarwa. Ya jaddada cewa samun ingantaccen kiwon lafiya muhimmin ginshiƙi ne na rayuwar al’umma, kuma bai kamata rashin ƙarfi ko ƙarancin hali ya zama dalilin hana mutum samun kulawar lafiya ba.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, ciki har da ACG Ahmad Garba Karaye, Kwanturola na Shiyya ta B; DCF Aminu Amadu, Kwanturola na Jihar Kaduna; da ACF Adamu Mukhtar Abdullahi, Kwanturola na Yankin Zaria. Haka kuma, ‘yan majalisar dokokin Jihar Kaduna masu wakiltar Zaria City da Zaria Kewaye, da sauran manyan baki da shugabanni sun halarci taron.
A wani ɓangare na ayyukan yau, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya kuma halarci wani shirin tallafa wa al’umma da Mataimakin Shugaban Ma’aikata (Bangaren Gudanarwa) na Kakakin Majalisar Wakilai, Malam Iliyasu Balarabe, ya ɗauki nauyin shiryawa. An gudanar da shirin a babban dakin taro na Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Zaria.
Shirin ya ƙunshi rabon babura masu amfani da wutar lantarki guda 15, bayar da guraben tallafin aikin Umrah guda 12, da kuma tallafin kuɗi ga ƙungiyoyin mata da matasa, domin ƙarfafa tattalin arziƙinsu, bunƙasa ƙungiyoyinsu da inganta hanyoyin samun abin dogaro da kai.
Injiniya Jaga ya yaba wa Malam Iliyasu Balarabe bisa wannan kyakkyawan tunani da kulawa da ya nuna ga al’ummar Zaria, yana mai cewa irin wannan taimako na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa rayuwar jama’a da samar musu da damammaki na ci gaba.
Read also: Oversight: Speaker Abbas inspect some projects in his constituency.
A ƙarshe, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da haɗa hannu da shugabannin siyasa, abokan hulɗa da sauran masu ruwa da tsaki domin jawo muhimman ayyukan ci gaba, ƙarfafa hukumomin gwamnati da inganta rayuwar al’ummar Zaria.
Ya kuma kara da cewa ci gaba ba nauyin mutum ɗaya ba ne, illa alhakin kowa ne, kuma ta hanyar haɗin kai, kyakkyawar manufa da shugabanci nagari ne za a iya cimma muradun ci gaban al’umma.






