Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria, Hon. Injiniya Jamil Ahmad Muhammad Jaga, a yau ya yi wata fitowar siyasa ta musamman a Kaduna, tare da rakiyar dimbin ‘ya’yan jam’iyya, magoya baya da abokan tafiyar siyasa daga Zaria, domin halartar ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa da na Gwamnan Jihar Kaduna na Jam’iyyar APC, tare da ƙaddamar da kwamitin gudanar da yaƙin neman zaɓen, wanda aka gudanar a filin wasa na Kaduna Township Stadium, Kaduna.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Galadima Ishaq Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria Shawara kan Yaɗa Labarai (Chief Press Secretary), Ofishin Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria ya baiwa manema labarai.
Read also: GOV. LAWAL PLEDGES MORE PROJECTS AS APC CAMPAIGN STORMS SHINKAFI LGA
Ya ce Shugaban ya kasance tare da Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, CON; Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, GCON; da sauran shugabannin jam’iyyar APC, masu ruwa da tsaki, dubban ‘ya’yan jam’iyya da magoya bayanta.
Wannan babban taro ya zama wata muhimmiyar dama ga shugabannin jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da magoya baya wajen sake jaddada amincewarsu da jagorancin APC da kuma goyon bayansu ga ‘yan takarar jam’iyyar a zaɓukan da ke tafe a shekar 2027.
Haka zalika, taron ya haɗa manyan jiga-jigan jam’iyya da magoya bayanta daga sassa daban-daban na Jihar Kaduna, lamarin da ya nuna haɗin kai da haɗin gwiwar mambobin jam’iyyar wajen gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe.
Read also: Campaign Train: Zulum Storms Mafa, Dikwa, Gamboru Ngala to Rousing Reception
Da yake bayyana muhimmancin taron, Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria, Jaga, ya sake tabbatar da goyon bayansa ga jagorancin APC, tare da bayyana goyon bayansa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu; Gwamna Uba Sani; ‘yan takarar Sanatoci na jam’iyyar; ‘yan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya, da kuma ‘yan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna.
Ya jaddada cewa, yaƙin neman zaɓen jam’iyyar zai ta’allaka ne kan nasarorin da aka samu, ayyukan raya ƙasa da ake iya tabbatarwa, da kuma ƙoƙarin ci gaba da inganta rayuwar al’umma tare da ƙara samar da ribar dimokuraɗiyya ga al’umma.
Haka kuma, Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria ya yi kira ga ‘ya’yan APC, magoya bayan jam’iyyar da al’ummar Zaria baki ɗaya da su ci gaba da kasancewa cikin lumana, jajircewa da haɗin kai, tare da taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da harkokin dimokuraɗiyya.
Wani abin lura na musamman a wannan fitowar shi ne yadda dimbin ‘ya’yan jam’iyya, magoya baya da abokan tafiyar siyasa suka raka Shugaban daga Zaria zuwa Kaduna domin halartar wannan babban taro. Shugaban ya bayyana matuƙar godiyarsa bisa wannan nuna goyon baya, haɗin kai da jajircewa da suka ci gaba da yi masa, tare da addu’ar Allah Ya dawo da kowa gida lafiya.
Read also: MY GOV’T HAS PROJECTS WORTH ₦109 BILLION IN MARU LGA, GOV. LAWAL DECLARES DURING APC CAMPAIGN RALLY
Kasancewar Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria a wannan babban taro ya ƙara bayyana irin ci gaba da taka rawa a harkokin siyasa wajen ƙarfafa haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a faɗin Zaria da sauran sassan jihar.
An kammala taron ne da kira ga ci gaba da haɗin kai, zaman lafiya da kuma himmatuwa wajen gudanar da harkokin siyasa cikin lumana, yayin da jam’iyyar APC ke ci gaba da shirye-shiryen yaƙin neman zaɓenta a faɗin Jihar Kaduna.






