Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, ya yi kira ga ’yan siyasa da al’ummar jihar da su jajirce wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2027, yana mai bayyana taken “Girmanka Akwantinka.”
Sanarwar manema labarai da kakakin Dan takarar Gwamna jihar Gombe Ibrahim Sani Shawai ya bayar ya ce Dr. Gwamna ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin ganawa tare da kaddamar da mambobin ƙungiyar Sarkin Doka Volunteer Support Group a birnin Gombe, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai, jajircewa da haɗa ƙarfi wajen cimma manufofin jam’iyyar APC
Read also: Kano Opposition Governorship Candidates Accuse APC, Incumbents Of Suppressing Dissenting Voices
Read also: A4A Elders More Relevant to Communities Than ACF Elders, Says Jadda Garko
Sardaunan na Gombe Ya kuma buƙaci mambobin ƙungiyar da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma da gudanar da ayyukan wayar da kai a matakin ƙananan hukumomi da unguwanni domin ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓen mai zuwa.
A yayin jawabin maraba uban kungiyyar, Sarkin Dokan Gombe, Alh Muhammad Adamu Abubakar ya ce sun kirkiro wannan kungiyyar ne don tallata APC da kuma yan takararta a jihar Gombe.
Ya kara da cewa samun nasarar jam’iyyar APC na buƙatar haɗin kai da gudunmawar kowane ɗan jam’iyya da magoya bayanta, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da jajircewa wajen wannan manufa.





