Daga Yahaya Mahi Na Malam Babba
Read also: Gov. Radda Urges Renewed Hope Food Aid Beneficiaries to Feed Their Families
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar yau Lahadi ta ƙone dakunan kwanan ɗalibai guda uku a Makarantar Tsangayar Mahiyya Global Academy, da ke unguwar Samaru a garin Kaura Namoda, Jihar Zamfara.
Read also: GROUP PRAYS FOR SPEEDY RECOVERY OF ABDULSALAMI, SEN. MUSA
Gobarar ta lalata kayayyakin ɗalibai da dama, ciki har da gadajen kwanan ɗalibai guda 60, katifu, zanunan shimfiɗar katifa, tufafi, littattafan karatu da kuma kayan abinci.
Sai dai, an yi sa’a, babu asarar rai ko wani rahoton jikkata sakamakon gobarar, domin lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ɗaliban suke cikin azuzuwan karatu na safe.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a san ainihin musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai wasu na danganta faruwar lamarin da yanayin hunturu da ake ciki, wanda a wannan lokaci ake yawan samun rahotannin tashin gobara a wurare daban-daban.
Read also: Speaker Abbas attracts, commissions two power projects in Soba, lays foundation for others
A halin da ake ciki, Hukumar Kashe Gobara ta yankin Kaura Namoda na ci gaba da wayar da kan al’umma kan muhimmancin ɗaukar matakan kariya daga gobara, tare da bin ƙa’idojin tsaro domin rage haɗarin tashin gobara a muhallan jama’a.
An kuma shawarci al’umma da su riƙa yin taka-tsantsan tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyinsu daga haɗarin gobara.




