Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jinjina wa sarakunan gargajiya da shugabannin jam’iyyar APC da zababbun jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin Yankin Funtua bisa goyon bayan da suka nuna wa jam’iyyar APC a yayin tarukan yaƙin neman zaɓen Tinubu-Dikko na 2027.
Gwamna Radda, wanda kuma shi ne mai kula da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu a jihar, ya bayyana cewa irin tarbar da aka yi wa tawagar kamfen a ƙananan hukumomi goma sha 11 na yankin abin a yaba ne ƙwarai.
Ƙananan hukumomin sun haɗa da Funtua, da Sabuwa, da Faskari, da Dandume, da Bakori, da Danja, da Kafur, da Kankara, da Malumfashi, da Musawa da kuma Matazu.
Gwamnan ya ce:
“Ina miƙa godiyata ta musamman ga sarakunanmu na gargajiya, da shugabannin jam’iyya,da zababbun jami’an gwamnati, waɗanda aka naɗa, da shugabannin al’umma, da ƙungiyoyin matasa da mata, da masu buƙata ta musamman, da dukkan magoya bayanmu bisa haɗin kai da gagarumin goyon bayan da suka ba mu a duk tsawon wannan yaƙin neman zaɓe.”
Ya ƙara da cewa irin himma da haɗin kan da aka nuna a faɗin yankin sun ƙara masa kwarin gwiwa kan azamar al’umma ta yin aiki tare domin cimma muradun da suke da su.
A cewarsa:
“Ƙarfin halinku, haɗin kanku da jajircewarku wajen tsayawa kan abin da kuka yi imani da shi sun ba mu dalilai masu yawa na kasancewa da kyakkyawan fata. Na ji daɗin irin haɗin kai da kuma ƙwazon da kuka nuna a dukkan tarurrukan da muka gudanar.”
Gwamna Radda ya bayyana cewa kamfen ɗin, wanda aka fara a Funtua aka kuma kammala a Matazu, ya ba shi damar ganawa da al’umma ido-da-ido, ƙarfafa tsarin jam’iyya daga tushe, tare da gabatar da nasarorin da gwamnatinsa ta samu a gaban jama’a.
Read also: NewsDirect Crowns Governor Radda Nigeria’s Best Security Governor
Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa irin wannan yanayi na haɗin kai da goyon baya zai ci gaba, har ma ya ƙaru a Yankin Daura.
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyya da magoya bayanta da kada su yi sakaci ko su yi ƙasa a gwiwa, maimakon haka su ci gaba da wayar da kan jama’a daga tushe, su ƙarfafa haɗin kansu, tare da yin aiki a matsayin iyali guda domin samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a babban zaɓen shekarar 2027.


