Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) ta amince da ƙarin kuɗi naira biliyan 130 domin gyara da inganta makarantun horas da jami’an ’yan sanda a faɗin Najeriya, lamarin da ya kai jimillar kuɗin shirin zuwa naira biliyan 230. Haka kuma, majalisar ta amince da wasu manyan ayyukan raya ƙasa guda biyu da za a samar musu da tallafin rancen Bankin Duniya na dala miliyan 850 domin ƙarfafa shirin yaƙi da bala’o’i da inganta rayuwar yara ƙanana.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Matakan na daga cikin muhimman matsayar da aka cimma a taron NEC karo na 162 da aka gudanar ranar Litinin. Kwamitin musamman da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ke jagoranta ya bayyana cewa ana gudanar da aikin gyaran cibiyoyin horas da ’yan sanda a wurare 13, inda aka kammala kashi 30 cikin 100 na aikin. Ana sa ran ƙarin kuɗin zai hanzarta aikin tare da ƙarfafa shirin ɗaukar sabbin jami’an ’yan sanda 50,000.
Read also: EXECUTIVE COUNCIL MEETING,ENGR JAGA CHAIRS 19 COUNCIL MEETING,FLAGS OFF NPC E-REGISTRATION IN ZARIA.
A ɓangaren tattalin arziki kuwa, Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya shaida wa majalisar cewa tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin 100 a zangon na biyu na shekarar 2026, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba, mafi ƙarancin mataki tun watan Satumban 2020. Haka kuma, ya bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙasa ta kai dala biliyan 54.87 zuwa ranar 12 ga Nuwamba, 2026.
Read also: Over 5,000 People Benefits From German Supported Project in Kaduna
Majalisar ta kuma amince da shirin ARISE-Nigeria mai darajar dala miliyan 350, wanda Bankin Duniya zai tallafa wa, domin taimaka wa ƙasar wajen shiryawa da tinkarar ambaliyar ruwa, fari, gobara da sauran bala’o’i. Haka kuma, an amince da shirin bunƙasa yara ƙanana a faɗin jihohi 36 da Abuja, wanda ake sa ran zai samu tallafin dala miliyan 500 daga Bankin Duniya da ƙarin tallafin dala miliyan 30 daga Global Financing Facility, domin inganta kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi da kariyar yara.
Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce nasarar gyare-gyaren tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa za ta dogara ne da gina ƙungiyoyi da cibiyoyi masu ƙarfi da za su tabbatar da dorewar nasarorin. Ya kuma buƙaci gwamnonin jihohi su ƙarfafa rajistar katin shaida na ƙasa, tare da aiwatar da tsarin fansho na ma’aikata. Daga ƙarshe, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi wajen tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun amfani al’umma.





