Najeriya da Indiya sun amince da ƙarfafa dangantakar tattalin arzikinsu, yayin da Indiya ta nuna sha’awar sake ƙara sayen ɗanyen man fetur daga Najeriya.
An cimma matsayar ne a wata ganawar ƙasashen biyu tsakanin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Firaministan Indiya, Narendra Modi, a gefen taron shugabannin ƙasashen BRICS da aka kammala a New Delhi.
Read also: NewsDirect Crowns Governor Radda Nigeria’s Best Security Governor
Cinikin Najeriya da Indiya ya kai dala biliyan 14.95 a shekarar kuɗi ta 2021 zuwa 2022, kafin ya ragu sakamakon raguwar sayen ɗanyen man Najeriya da Indiya ke yi. Cinikin ya sauka zuwa dala biliyan 7.13 a 2024 zuwa 2025, kafin ya farfaɗo zuwa kusan dala biliyan 9 a 2025 zuwa 2026.
Read also: FORCE COMMANDER, CÔTE D’IVOIRE CONTINGENT RECEIVE ECOWAS PEACEKEEPING MEDALS IN GUINEA-BISSAU
Shettima ya ce Najeriya za ta duba buƙatar Indiya ta sake ƙara sayen ɗanyen man fetur, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jawo ƙarin zuba jari da ƙulla dangantakar tattalin arziki da za ta taimaka wajen faɗaɗa ƙarfin samar da kayayyaki a ƙasar.
Ƙasashen biyu sun kuma tattauna faɗaɗa haɗin gwiwa a fannonin makamashi mai tsafta, wutar lantarki, kiwon lafiya, bunƙasa ƙwarewar ma’aikata, fasahar hada-hadar kuɗi da sauran sabbin fannoni. Firaminista Modi ya kuma nuna godiya ga Najeriya bisa kyakkyawar tarbar da take bai wa ɗimbin ’yan ƙasar Indiya da ke zaune da gudanar da harkokin kasuwanci a Najeriya.
Sabuwar Nigeria.

