Gagarumar tarbar da aka yi wa ɗan takarar gwamnan Gombe na APC, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, a unguwar Pantami ta rikide zuwa babban taron siyasa, inda maza da mata, matasa da dattawa suka fito domin ganinsa da kuma tarbarsa.
Cikin wata sanarwar manema labarai da Ibrahim Sani Shawai Mai magana da yawun Dan Takarar Gwamna na APC a Jihar Gombe, Dr Jamil Gwamna ya bayar ya ce unguwar Pantami da ke cikin birnin Gombe ta dauki hankalin jama’a a ranar Lahadi, yayin da ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, ya samu tarba mai armashi daga ɗimbin al’ummar yankin.
Read also: GOMBE 2027: Traders, Artisans, Endorse Gwamna, Pledge Grassroots Mobilisation for APC
Dr. Gwamna ya kai ziyara unguwar ne domin ƙaddamar da sabon ofishin kamfen na APC, wanda Alhaji Abdulhamid Jibrin ya buɗe, da nufin ƙarfafa ayyukan yaɗa manufofin jam’iyyar da tattara magoya baya daga mataki na Kasa wato (grassroots)
Sai dai abin da ya fi ɗaukar hankali a wajen taron shi ne yadda ɗimbin jama’a, ciki har da maza da mata, matasa, dattawa da yara, suka fito domin ganin ɗan takarar, lamarin da ya sauya taron buɗe ofishin zuwa wata babbar dama ta nuna goyon baya da sha’awar siyasar Sardaunan na Gombe.
Al’ummar yankin sun nuna farin cikinsu da zuwan Dr. Gwamna, yayin da waɗanda suka samu damar yin jawabi a wajen taron suka bayyana ra’ayinsu cewa shi ne ɗan takarar da suka yi imanin ya fi cancanta da dacewa da shugabancin jihar Gombe.
A nasa jawabin, Dr. Jamil Gwamna ya yaba da tarba ta musamman da al’ummar Pantami suka yi masa, inda ya nuna godiya bisa karamci, girmamawa da goyon bayan da suka nuna masa.
Read also: ADC-PCC DISMISSES KWANKWASO’S RESPONSE AS DIVERSIONARY
Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da hulɗa da al’umma kai tsaye, domin fahimtar buƙatunsu da ƙarfafa haɗin kai wajen samar da shugabanci mai amfani ga jama’a.
Taron ya kasance wani ɓangare na ƙoƙarin APC na faɗaɗa ayyukan kamfen da ƙarfafa hulɗa da al’umma a matakin ƙasa, yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.











