Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake aiwatarwa na aza harsashin gina Nijeriya da tattalin arziki mai ƙarfi. Ya kuma yi kira ga mata da su taimaka wajen bayyana manufofin gwamnati ga ’yan ƙasa.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, lokacin da jagorar ƙungiyar “Women of Influence for Tinubu 2027” ta ƙasa, Hajiya Hauwa Farouk Ibrahim, ta jagoranci tawagar ƙungiyar zuwa ziyarar girmamawa a ma’aikatar.
Read also: Gov. Yusuf Unveils APC 2027 Presidential and Gubernatorial Campaign Council
Ya ce cire tallafin man fetur da haɗa farashin canjin kuɗin waje tsauraran matakai ne, to amma wajibi ne domin magance matsalolin tattalin arziki da suka daɗe suna addabar ƙasar nan, daidaita harkokin kuɗaɗen gwamnati da samar da damarmakin cigaba mai ɗorewa.
A cewar ministan, sauye-sauyen sun ƙara yawan kuɗaɗen da gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi za su iya amfani da su wajen gina ababen more rayuwa, samar da muhimman ayyuka da aiwatar da sauran shirye-shiryen cigaba.
Ya ce: “Waɗannan matakai masu wuya ne, amma an ɗauke su ne domin amfanin ƙasar mu.”
Ya buƙaci ƙungiyar da ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a, ta hanyar bayyana dalilan da suka sa aka aiwatar da sauye-sauyen, manufofin su da kuma damarmakin da za su samar domin cigaban ƙasa.
Idris ya sake jaddada aniyar ma’aikatar ta yin aiki tare da ƙungiyoyin da ke taimaka wa jama’a su fahimci manufofin gwamnati. .
Ya amince da buƙatar ƙungiyar ta naɗa shi a matsayin majiɓincin ta, tare da alƙawarin naɗa jami’in hulɗa da zai taimaka wajen daidaita ayyukan haɗin gwiwa.
Tun da farko, Hajiya Hauwa ta ce an kafa ƙungiyar “Women of Influence for Tinubu 2027” ne domin tattara mata ’yan Nijeriya wuri guda, tare da amfani da jagorancin su da tasirin su a cikin al’umma wajen tallafa wa cigaban ƙasa da gwamnatin Tinubu.
Read also: Governor Radda Thanks Tinubu Approval of Transmission Substation for Mashi
Ta ce ƙungiyar ta fara gudanar da ayyukan ta a Jihar Kano, kuma tana faɗaɗa su ta kafafen sadarwa na zamani da shirye-shiryen da ake gudanarwa a cikin al’umma domin hulɗa da mata da sauran ’yan ƙasa a faɗin Nijeriya.
Hajiya Hauwa ta gode wa ministan bisa karɓar tawagar ƙungiyar, tare da neman haɗin gwiwar ma’aikatar wajen ƙarfafa shirye-shiryen wayar da kan jama’a da hulɗa da su.
