Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar NPERA Ta 2026
    News

    Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar NPERA Ta 2026

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 15, 20262 Mins Read
    FB IMG 1786781759348
    FB IMG 1786781759348

    Daga Aliyu Samba

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Tattalin Arziƙin Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPERA) ta shekarar 2026, matakin da ya bai wa Majalisar Kula da Masu Safarar Kaya ta Najeriya (NSC) cikakken ƙarfin doka wajen gudanar da ayyukan sa ido da daidaita harkokin tattalin arziƙin tashoshin jiragen ruwa.

    Babban Sakataren NSC, Dakta Pius Akutah, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tantance, inda ya gode wa Shugaba Tinubu bisa sanya hannu kan dokar.

    Masana harkokin sufurin jiragen ruwa sun ce dokar ta buɗe sabon babi wajen samar da cikakken mai kula da harkokin tattalin arziƙin tashoshin jiragen ruwa, wanda zai samu ikon ɗaukar mataki kan masu gudanar da ayyukan tashoshin da suka karya ƙa’idoji.

    Masanin harkokin ruwa, Dakta Eugene Nweke, ya ce dokar ta kasance sakamakon ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi tun bayan bai wa kamfanoni damar gudanar da tashoshin jiragen ruwan Najeriya a shekarar 2006.

    Ya ce a shekarar 2014 Gwamnatin Tarayya ta bai wa NSC matsayin mai kula da harkokin tattalin arziƙin tashoshin jiragen ruwa na wucin gadi, yayin da ake jiran samar da cikakkiyar dokar da za ta ba da wannan iko.

    A cewarsa, kafin sanya hannu kan sabuwar dokar, NSC na gudanar da wasu ayyukan sa ido bisa manufofin gwamnati da kuma wata sanarwar gwamnati ta shekarar 2015.

    Ya ce sabuwar dokar ta bai wa hukumar da za ta gudanar da aikin ikon kula da kuɗaɗen fito da kaya, farashi da caji, gasa tsakanin masu samar da ayyuka da kuma bayar da lasisin gudanar da ayyukan tashoshin jiragen ruwa.

    Dokar ta kuma tanadi hanyoyin warware takaddamar kasuwanci da ka iya tasowa a harkokin tashoshinjiragen ruwa.

    Sabuwar Nigeria.

    dokar jiragen pbat ruwa sufurin
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleHukumar Aikin Hajji ta kasa,NAHCON ta Sanar Da Kudin kujerar Hajjin 2027, Ta Kayyade Ranar Ƙarshe Ta Biyan Kuɗin Maniyyata
    Next Article Shugaba Tinubu Ya Yi Horon ,Da A Tabbatar Da Gudanar Da Zaɓen Jihar Osun Cikin Lumana Da Adalci

    Related Posts

    News

    NPF ARRESTS, REPATRIATES CHADIAN FUGITIVE WANTED FOR MURDER IN N’DJAMENA

    August 15, 2026
    News

    Seme Customs Halts Expired Food Entry, Hands Over Seized Explosives to Police

    August 15, 2026
    News

    SETTING THE RECORD STRAIGHT: HOW GOVERNOR INUWA YAHAYA IS ADDRESSING AGE-LONG WATER CHALLENGE IN GOMBE

    August 15, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026157 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.