Shugaban Karamar Hukumar Matazu. Hon. Shamsuddeen Muhd Sayaya ( Sarkin yakin Matazu ii) ya ziyarci hedkwatar Yan sanda ta Karamar Hukumar Matazu domin mika ta’aziya na rashin bayin Allah guda biyu da Yan binga suka kashe daya Jami’in Dan sanda Mai mikamin kofur Sulaiman Sai daya fara hula da suka harba akan hanyar zuwa Karadu’a.
Read also: Kwankwaso Should Stop Dragging Gov. Yusuf into His EFCC Troubles, Kano Government Declares
Wannan Na kunshe ne cikin wata sanarwar da Jamin yada labarai Na karamar hukumar matazu Mansir Bala ya rabama manema labarai.
Read also: Nigeria’s future lies with young population—Speaker Abbas
Hon. Shamsuddeen Muhd Sayaya yace yazo hedkwatar domin jajantama al’umma halin firgichi da muka tashi dashi haka kuma ya ziyarci garin Sayaya domin jajantama wadanda suka rasa dukiyoyin su ya kuma duba Asibitin kula da kiwon Lafiya a matakin farko da suka sama wani bangare na Asibitin wuta.
Hon. Shamsuddeen Muhd ya kuma godema Maigirma Gwamnan Jihar Katsina. Mal. Dikko Umar Radda PhD, CON, dajin abinda ke faruwa ya tashi tare da Yan tawagar shi zuwa garin Sayaya domin nuna damuwa da halinda al”umma suka sami kansu na harin Yan ta’adda.
Read also: COAS JOINS PRESIDENT TINUBU, CDS, SERVICE CHIEFS IN PAYING LAST RESPECTS TO FALLEN NAF 931 CREW
Haka kuma Hon. Shamsuddeen Muhd yayi kira ga al’umma da a cigaba da gudanar da addu’oi na Musanman domin neman Allah ya tabbatar mana da zaman Lafiya Mai dorewa yace zasu cigaba da daukar Matakai tare da masu ruwa da tsaki domin ganin hakan bai kara faruwa ba da izinin Allah

