Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»News»SUFURIN JIRGIN KASA: Shugaba Tinubu ya ƙara kaimi wajen kammala manyan ayyukan jirgin ƙasa a Arewacin Najeriya
    News

    SUFURIN JIRGIN KASA: Shugaba Tinubu ya ƙara kaimi wajen kammala manyan ayyukan jirgin ƙasa a Arewacin Najeriya

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanNovember 8, 20264 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1794162672937

    ● Za a ƙaddamar da layin dogo na Kaduna zuwa Kano a ranar 3 ga Disamba

    ● Aikin layin dogo na Kano–Katsina–Maradi ya kai kashi 70 cikin 100 na kammalawa

    Read also: Over 5,000 People Benefits From German Supported Project in Kaduna

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara kaimi wajen ganin an kammala manyan ayyukan layukan dogo da ake gudanarwa a Arewacin Najeriya, inda ake shirin ƙaddamar da layin dogo na Kaduna zuwa Kano a ranar 3 ga Disamba, 2026.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Aikin layin dogo mai tsawon kilomita 203 na Kaduna–Zariya–Kano, wanda yana daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gada da kuma waɗanda take mayar da hankali a kansu, ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammaluwa.

    Haka kuma, aikin layin dogo na Kano–Katsina–Maradi, mai tsawon kilomita 400, ya kai kashi 70 cikin 100 na kammaluwa.

    Idan Za a iya tunawa dai, lokacin da Shugaba Tinubu ya karɓi ragamar mulki a shekarar 2023, aikin layin dogo na Kano–Katsina–Maradi bai wuce kashi 5 cikin 100 na kammaluwa ba, yayin da na Kaduna–Kano bai kai kashi 30 cikin 100 ba.

    Wannan ci gaba na nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na faɗaɗa hanyoyin sufuri na jirgin ƙasa, inganta haɗin kai tsakanin yankuna da sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji da jigilar kayayyaki a cikin Najeriya da ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita.

    Layin dogon na Kaduna–Kano, wanda yake ci gaban tsohon layin dogo na Abuja–Kaduna, zai samar da cikakkiyar hanyar jirgin ƙasa da za ta haɗa Abuja, Kaduna, Zariya da Kano, tare da ƙarfafa harkokin sufuri tsakanin manyan cibiyoyin kasuwanci na Arewacin Najeriya.

    A wani mataki na tabbatar da ingancin ayyukan, wata tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Injiniya Funso Adebiyi, ta gudanar da bincike a kan ayyukan bisa umarnin Shugaba Tinubu.

    Read also: INEC ready for Saturday’s mock election in Yobe, declares 158,652 PVCs unclaimed

    Tawagar ta nuna gamsuwa da ingancin ayyukan gine-ginen, musamman shimfiɗar layin dogo, magudanan ruwa, kariyar tuddai, shimfiɗa duwatsu da kuma matakan ƙarfafa ƙasar da aka bi domin tabbatar da ɗorewar aikin.

    A yayin ziyarar, tawagar ta kuma gudanar da gwajin tafiyar jirgin ƙasa daga Jaji a Jihar Kaduna zuwa Kano, domin tantance ingancin layin dogon da aka kammala da kuma jin daɗin fasinjoji yayin tafiya.

    Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin cewa a gaggauta warware dukkan matsalolin da suka shafi mallakar filaye da biyan diyya a cikin birnin Kaduna, domin tabbatar da kammala dukkan sassan hanyar jirgin ƙasan daga Abuja zuwa Kano.

    Daga cikin ayyukan da ake shirin ƙaddamarwa a ranar 3 ga Disamba, 2026, akwai ɓangaren layin dogo mai tsawon kilomita 190 daga Jaji zuwa Kano, daga cikin jimillar kilomita 205 na aikin Kaduna–Kano.

    Haka kuma, za a ƙaddamar da ɓangaren aikin Kano–Maradi mai tsawon kilomita 250, wanda ya haɗa da Dawanau, Kano, Kazaure, Daura da Katsina.

    Ana sa ran da zarar layin dogo na Kaduna–Kano ya fara aiki, zai sauƙaƙa jigilar fasinjoji, bunƙasa harkokin kasuwanci tare da samar da wata hanya ta daban ga matafiya da ke amfani da manyan hanyoyin mota a ɗaya daga cikin yankunan kasuwanci mafiya muhimmanci a Arewacin Najeriya.

    Haka nan, layin dogo na Kano–Katsina–Maradi, wanda ya kai kashi 70 cikin 100 na kammalawa, zai ƙara ƙarfafa zirga-zirgar sufuri da kasuwanci tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da buɗe sabbin damarmakin tattalin arziki ga al’ummomin da ke kan hanyar.

    Read also: Just In: PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU SIGNS FOUR BILLS INTO LAW AS PRESENTED TO HIM BY THE HOUSE OF REPRESENTATIVES.

    Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa, bisa ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za a tabbatar da kammala dukkan ayyukan samar da ababen more rayuwa da ake gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan bisa jadawalin da aka tsara.

    Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na mayar da manyan ayyukan sufuri tamkar ginshiƙin bunƙasa tattalin arziki, haɗa yankuna da samar da sabbin damarmakin ci gaba ga al’ummar Najeriya.

    FB IMG
    FB IMG 1794162691331
    FB IMG
    FB IMG 1794162684305
    FB IMG
    FB IMG 1794162678388
    FB IMG
    FB IMG 1794162661635
    FB IMG
    FB IMG 1794162667244
    FB IMG
    FB IMG 1794162672937
    3 Commissioning dec for Kaduna kano liner rail
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGo to Your Polling Unit,’ Zulum Tells Borno APC as He Inaugurates 2027 Campaign Council
    Next Article KADUNA STATE LOCAL GOVERNMENT SERVICE COMMISSION BEGINS PROMOTION EXERCISE FOR LOCAL GOVERNMENT STAFF.

    Related Posts

    News

    PRESIDENT TINUBU MOURNS FORMER LAGOS DEPUTY GOVERNOR SEN. IDIAT ADEBULE

    November 28, 2026
    News

    Just In: PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU SIGNS FOUR BILLS INTO LAW AS PRESENTED TO HIM BY THE HOUSE OF REPRESENTATIVES.

    November 28, 2026
    Politics

    Kano Opposition Governorship Candidates Accuse APC, Incumbents Of Suppressing Dissenting Voices

    November 28, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.