Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»Health»TAB Medics Ta Kai Tallafin Lafiya Ga Iyalai 200 a Jihar Kano
    Health

    TAB Medics Ta Kai Tallafin Lafiya Ga Iyalai 200 a Jihar Kano

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanNovember 14, 20263 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1794683811028

    Shirin TAB Medics (Tinubu Abba Barau Medics) ya gudanar da aikin tallafa wa marasa lafiya kyauta ta fuskar gwaji da maganin cutar zazzabin cizon sauro ga mazauna mazabar Babban Giji da ke ƙaramar hukumar Tarauni a birnin Kano.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce aikin, wanda aka gudanar a ranar Asabar a makarantar Hausawa Special Primary School, ya samu halartar iyalai sama da 200, inda aka yi musu gwajin cutar zazzabin cizon sauro, aka ba marasa lafiyar magunguna tare da raba musu sange mai maganin sauro.

    Read also: NANNM, ABUTH ZARIA CHAPTER, INAUGURATES NEWLY ELECTED EXECUTIVE COUNCIL

    Da yake jawabi yayin shirin, wanda ya assasa TAB Medics, Aliyu Samba, ya ce wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarinsa na taimakawa wajen ganin an kawar da cutar zazzabin cizon sauro a Jihar Kano, ta hanyar samar wa iyalai damar samun gwaji, magani da hanyoyin kariya kyauta.

    Samba ya bayyana cewa shirin an tsara shi ne domin kai muhimman ayyukan kula da cutar zuwa ga al’ummomin da ke buƙatar tallafi, tare da rage nauyin da cutar ke ɗora wa iyalai.

    Ya ƙara da cewa shirin zai haɗa da bayar da maganin zazzabin cizon sauro kyauta, gwajin cutar, raba sange mai maganin sauro da kuma matakan yaƙi da sauro, ciki har da fesa maganin kashe sauro.

    A cewarsa, manufar shirin ita ce tabbatar da cewa iyalai, musamman talakawa, sun samu damar kariya da maganin cutar ba tare da wani ƙalubalen kuɗi ba.

    Read also: ABUTH COLLEGE OF NURSING RECORDS 98% PASS IN NURSING AND MIDWIFERY COUNCIL EXAMINATION (BASIC NURSING).

    Ya kuma bayyana cewa za a faɗaɗa shirin zuwa wasu al’ummomi domin inganta lafiyar iyalai da taimakawa wajen ganin an samu Kano marar cutar zazzabin cizon sauro.

    A nasa jawabin, Mai Unguwar Hausawa Loko, Malam Bala Sa’idu, wanda ya yi magana a madadin waɗanda suka amfana da shirin, ya nuna godiyarsa ga wanda ya assasa shirin bisa kawo irin wannan tallafi ga al’ummarsu.

    “Ina matuƙar godiya ga Aliyu Samba bisa kawo wannan kyakkyawan shiri gare mu. Ba kowa ne yake samun damar tuna al’ummarsa da kuma yi musu irin wannan tallafi ba.”

    Ya kuma yi addu’ar Allah Ya saka wa shugabannin da Aliyu Samba ke aiki tare da su, tun daga Shugaban Ƙasa har zuwa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da Gwamnan Kano, bisa goyon baya da ƙarfafa shi har ya kai ga kawo wannan tallafi ga al’ummarsu.

    Haka kuma, Sakataren APC na mazabar Babban Giji, Malam Shafiu, ya nuna godiyarsa a madadin shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.

    Read also: Gov. Abba K. Yusuf set to flag-off 2027 campaign sunday in Rogo

    Ya yaba da wannan tallafi, yana mai bayyana shi a matsayin gudummawa mai ma’ana wajen inganta samun ayyukan kula da lafiya a matakin ƙasa.

    Shirin na TAB Medics na daga cikin ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi wajen yaƙi da zazzabin cizon sauro ta hanyar rigakafi, gano cutar da wuri, bayar da magani da wayar da kan jama’a, tare da kai ayyukan lafiya kusa da al’umma.

    FB IMG
    FB IMG 1794683804261
    FB IMG
    FB IMG 1794683792055
    FB IMG
    FB IMG 1794683797502
    FB IMG
    FB IMG 1794683782101
    kano medical outreach table
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleCOAS, SERVICE CHIEFS REINFORCE MILITARY SOLIDARITY AT NDA 40TH REGULAR COURSE RETIREMENT
    Next Article Yoruba Community in Kano Endorses President Tinubu, Gov. Yusuf for Second Term

    Related Posts

    Politics

    Gov. Abba K. Yusuf set to flag-off 2027 campaign sunday in Rogo

    November 27, 2026
    Health

    NANNM, ABUTH ZARIA CHAPTER, INAUGURATES NEWLY ELECTED EXECUTIVE COUNCIL

    November 26, 2026
    Health

    ABUTH COLLEGE OF NURSING RECORDS 98% PASS IN NURSING AND MIDWIFERY COUNCIL EXAMINATION (BASIC NURSING).

    November 26, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026218 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.