Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya a ranar Laraba, bayan kammala ibadar Umara a birnin Makkah mai alfarma.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Jirgin shugaban ƙasar ya tashi daga filin jirgin saman Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da misalin ƙarfe 5:13 na yamma agogon Saudiyya, zuwa Abuja, babban birnin Najeriya.
Read also: NANNM, ABUTH ZARIA CHAPTER, INAUGURATES NEWLY ELECTED EXECUTIVE COUNCIL
Mataimakin Gwamnan Yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz Al Saud, tare da Jakadan Najeriya a Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo, da Babban Jami’in Ofishin Jakadancin Najeriya a Jeddah, Ambasada Muazam Ibrahim Nayaya, sun raka shugaban ƙasar zuwa filin jirgin saman.
Kafin tashinsa, Shugaba Tinubu ya gana da Mataimakin Gwamnan Makkah a taƙaice a fadar baƙi ta masarauta da ke filin jirgin saman.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata, shugaban ƙasar ya jagoranci tawagar Najeriya wajen gudanar da ibadar Umara, ciki har da ɗawafin Ka’aba.
Haka kuma, a ranar Lahadin da ta gabata, an ba Shugaba Tinubu damar shiga cikin Ka’aba, inda shi da wasu daga cikin tawagarsa suka gudanar da sallar raka’a biyu.
A yayin da yake cikin Ka’aba, shugaban ƙasar ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya azurta Najeriya da zaman lafiya mai ɗorewa, tsaro, haɗin kai da wadata. Ya kuma roƙi Allah ya ba shi shiriya, hikima da ƙarfin gwiwar ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima.
Haka nan, ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa Najeriya, shugabanninta da al’ummarta albarka, tare da fatan cewa bambancin da ke tsakanin al’ummar ƙasar zai zama tushen ƙarfi, haɗin kan ƙasa da wadata da kowa zai amfana da ita.
Gwamnatin ta ce ziyarar shugaban ƙasar zuwa Saudiyya ta ba shi damar yin tunani a kan al’amuran rayuwa, gode wa Allah da kuma yin addu’o’in neman zaman lafiya da ci gaban Najeriya, tare da sabunta ƙudurinsa na gina ƙasa mai zaman lafiya, haɗin kai da wadata.
Shugaba Tinubu ya kuma nuna godiya ta musamman ga Mai Kula da Masallatai Masu Alfarma Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman, bisa karamci da kyakkyawar tarbar da suka yi masa da tawagarsa, musamman damar shiga cikin Ka’aba domin gudanar da addu’o’i.
Shugaban ƙasar ya bar Saudiyya da sabunta imani, godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, da kuma ƙudurin ci gaba da aiwatar da shirin Renewed Hope Agenda, domin gina Najeriya mafi inganci ga dukkan ’yan ƙasarta.
Daga cikin tawagar shugaban ƙasar akwai mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, da gwamnonin jihohin Sokoto, Jigawa, Kaduna, Borno da Yobe, da sauran manyan jami’an gwamnati.

