Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»News»Tinubu Ya Bukaci A Sake Tsara Dokokin Duniya Don Tabbatar Da Adalci, Daidaito Da Wakilcin Kowa
    News

    Tinubu Ya Bukaci A Sake Tsara Dokokin Duniya Don Tabbatar Da Adalci, Daidaito Da Wakilcin Kowa

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanSeptember 14, 20262 Mins Read
    FB IMG 1789371309410
    FB IMG 1789371309410

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira da a gaggauta sake fasalin tsarin shugabancin duniya da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, yana mai cewa ya kamata tsarin ya kasance mai wakilci, adalci da kuma amsa bukatun sauye-sauyen tattalin arziki da yawan jama’a na duniya.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a taron shugabannin BRICS na 2026 da ke gudana a New Delhi, India, a cikin jawabin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya gabatar a madadinsa. Ya ce Najeriya na goyon bayan sake fasalin Majalisar Dinkin Duniya, musamman Kwamitin Tsaro, da kuma tsarin hada-hadar kudi na duniya domin su dace da yanayin duniya na yanzu.

    Read also: 2027: After Clerics, Barau Mobilises 3,405 Traditional Rulers in Kano for Tinubu, Abba, Other APC Candidates

    Read also: Tinubu Honours 25 Victims Of NAF 931 Aircraft Accident, Donates Houses, N100m To Each Deceased Family*

    Tinubu ya kuma bukaci a mayar da hadin gwiwar BRICS daga tattaunawa zuwa aiwatarwa, tare da samun sakamakon ci gaba da za a iya aunawa. Ya gayyaci masu zuba jari na kasashen waje da su yi amfani da damar zuba jari da ke Najeriya, yana mai bayyana kasar a matsayin kofar shiga babbar kasuwar Afirka karkashin yarjejeniyar African Continental Free Trade Area (AfCFTA).

    Read also: EXECUTIVE COUNCIL MEETING,ENGR JAGA CHAIRS 19 COUNCIL MEETING,FLAGS OFF NPC E-REGISTRATION IN ZARIA.

    Shugaban ya ce Najeriya na maraba da karin hadin gwiwa da kasashen BRICS a fannonin fasahar zamani, kamar Fasahar (AI), tsarin ayyukan gwamnati na dijital, harkokin fintech, sadarwa, tsaron yanar gizo, fasahar kere-kere, makamashi, noma, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da sarrafa ma’adanai masu muhimmanci. Ya ce Najeriya na son hadin gwiwar da zai taimaka wajen musayar fasaha, bunkasa masana’antu, samar da ayyukan yi da kuma gina jarin dan Adam.

    Tinubu ya jaddada cewa matasan Najeriya na daga cikin manyan kadarorin kasar, musamman saboda kirkire-kirkirensu da harkokin kasuwanci. Ya ce shirye-shiryen gwamnati kamar 3MTT, Project BRIDGE da shirye-shiryen AI na kasa na daga cikin kokarin bunkasa fasahar zamani da tattalin arzikin dijital, yana mai cewa ya kamata Afirka ta daina kasancewa a bayan fagen ci gaban duniya, ta koma sahun gaba wajen bunkasa tattalin arziki da kirkire-kirkire.

    FB IMG 1789371303255
    FB IMG 1789371303255
    FB IMG 1789371294591
    FB IMG 1789371294591
    FB IMG 1789371287296
    FB IMG 1789371287296
    FB IMG 1789371277808
    FB IMG 1789371277808
    FB IMG 1789371272391
    FB IMG 1789371272391
    brics India meeting message pbat Shettima
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGwamna Inaugurates Jamilu Solidarity Group Office in Gombe
    Next Article Second Term For Tinubu Defines The Spirit Of Justice and Fairplay-Gov. Buni

    Related Posts

    News

    Gwamna Commends Construction of 13 LCDA Secretariats, Pledges to Consolidate Gains

    November 28, 2026
    News

    Gov Inuwa Yahaya Hails Creative Industry as Platform for Youth Empowerment, Gombe’s Global Visibility

    November 28, 2026
    News

    Gov. Yusuf Commiserates with Yankifi Market Fire Victims in Kano

    November 28, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.