Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci al’ummar jihar Filato da su sake ba shi dama tare da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben 2027, yana mai cewa gwamnatinsa na kokarin magance matsalolin tsaro da inganta ayyukan raya kasa.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Tinubu ya yi wannan kira ne a babban gangamin yakin neman zaben APC na shiyyar Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a filin wasa na Zaria Road da ke Jos, mai daukar mutane 60,000. Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya da hadin kai ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila da al’adu ba.
Read also: Gov. Abba K. Yusuf set to flag-off 2027 campaign sunday in Rogo
Dangane da matsalar tsaro, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa kyamarorin sa ido da ya yi alkawarin samarwa jihar Plateau sun iso Najeriya, kuma nan ba da jimawa ba za a girka su. Ya kara da cewa jami’an tsaron gandun daji 1,000 da gwamnatin tarayya ta dauka aiki suna samun horo, kuma za su fara aiki bayan kammala horon domin taimakawa hukumomin tsaro wajen sa ido a dazuzzuka da sauran wuraren da ke da barazanar tsaro.
Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa shirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi na kan gaba a kokarin inganta tsaro a kasar.
Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya danganta ci gaban da ake samu a Filato da sauran sassan Najeriya da jagorancin Shugaba Tinubu, inda ya yabawa al’ummar jihar bisa gudunmawarsu a fannonin ilimi, noma, aikin soja, kasuwanci da wasanni.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jihar Plateau ta amfana da ayyukan gwamnatin tarayya da suka hada da hanyoyi, bataliyoyin sojoji guda biyu, rundunar Brigade da cibiyoyin kula da tsaro guda hudu. Ya kuma bayyana Tinubu a matsayin shugaban da ke cika alkawuransa, tare da bukatar al’umma su sake zabensa.
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon bayan gwamnatin tarayya a fannonin hanyoyi, ilimi da kiwon lafiya. Ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin samar da ayyukan yi ga matasa kusan 2,000 ta hanyar bai wa kamfanoni da kungiyoyi a Amurka da Turai damar daukarsu aiki ta yanar gizo. Ya kuma bayyana samar da cibiyar kula da tsaro mai amfani da fasahar zamani domin taimakawa wajen gano masu aikata laifuka, tare da kara motocin bas masu amfani da iskar CNG domin saukaka sufuri.
Read also: Governor Radda Assures APC Northwest Reconciliation Committee of Party Unity
Daraktan Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, Sanata Abdulaziz Yari, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, sun bukaci al’ummar Filato su sake zabar Tinubu, inda suka yaba da kokarin gwamnatin wajen tafiyar da tattalin arziki da samar da ayyukan ci gaba. Tsoffin gwamnonin jihar, Joshua Dariye da Simon Lalong, da tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Wase, da tsohuwar mataimakiyar gwamna, Pauline Tallen, sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa.
A yayin gangamin, Yilwatda ya kuma mika tutocin APC ga ‘yan takarar gwamna a Nasarawa, Aliyu Wadada, da Kwara, Yakubu Danladi, tare da bukatarsu da su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2027. Gangamin ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa, ministoci da masu rike da mukaman gwamnati.




