Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Zaratan Sojojin Nijeriya Sun Ceto Mutane 14 da Aka Yi Garkuwa da Su, Sun Kwato Dabbobi 281 da ’Yan Bindiga Suka Sace a Sakkwato
    Security

    Zaratan Sojojin Nijeriya Sun Ceto Mutane 14 da Aka Yi Garkuwa da Su, Sun Kwato Dabbobi 281 da ’Yan Bindiga Suka Sace a Sakkwato

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 6, 20262 Mins Read
    FB IMG 1786032176335
    FB IMG 1786032176335

    Daga Aliyu Samba

    Dakarun Rundunar Sojin Najeriya ta 8 Division Garrison sun ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su tare da kwato dabbobi 281 da wasu ’yan bindiga suka sace bayan sun kai hari ƙauyen Horo Birni da ke Ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.

    Wata majiya mai tushe a rundunar sojin ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda dakarun suka gaggauta kai ɗauki bayan samun kiran neman agaji daga mazauna yankin.

    Majiyar ta ce da isar sojojin, sun yi arangama da ’yan bindigar da ke tafiya da mutanen da suka yi garkuwa da su tare da dabbobin da suka sace daga ƙauyen.

    Ta bayyana cewa sojojin sun yi wa ’yan bindigar ruwan wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin ruɗani bayan sun samu raunukan harbin bindiga, suka bar mutanen da suka sace da kuma dabbobin.

    A cewar majiyar, sojojin sun yi nasarar ceto mutane 14 tare da kwato shanu 195, tumaki 84, rakuma biyu da kuma babura biyu.

    Ta ƙara da cewa gaggawar da sojojin suka yi wajen kai ɗauki ta taimaka wajen ceton rayuka da dukiyoyin al’umma, tana mai yabawa haɗin gwiwar jami’an tsaro da ya taimaka wajen nasarar aikin.

    Majiyar ta jaddada cewa dakarun sojin na ci gaba da kasancewa cikin shiri domin yaƙi da duk wani nau’in ta’addanci da laifuffuka, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken haɗin kai da kuma kai rahoton duk wani abin da ba su yarda da shi ba.

    FB IMG 1786032185970
    FB IMG 1786032185970
    FB IMG 1786032170632
    FB IMG 1786032170632
    big ceto mutane sojoji sokoto sun wasu
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticlePSC HANDS OVER 50,000 RECRUITED CONSTABLES TO POLICE FOR TRAINING
    Next Article COAS PLEDGES DEEPER NIGERIA–BURUNDI MILITARY TIES TO STRENGTHEN REGIONAL SECURITY

    Related Posts

    Security

    COAS PLEDGES DEEPER NIGERIA–BURUNDI MILITARY TIES TO STRENGTHEN REGIONAL SECURITY

    August 6, 2026
    Security

    PSC HANDS OVER 50,000 RECRUITED CONSTABLES TO POLICE FOR TRAINING

    August 6, 2026
    Security

    Gov. Idris Convenes Emergency Security Meeting to Strengthen Security

    August 6, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026280 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026237 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026216 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026161 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026157 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.