….Duk Wandanda Aka Kama Su Biya Diyya
Shugaban kungiyar Magnet For Peace Reconciliation and Youth Empowerment Foundation, Kwamared Mohammed Emegu, ya bayyana wa manema labarai cewa sun yi tir da Allah wadai da irin kisan Gillar da aka yi wa wata mata a garin Marabar Jos da ke karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna arewacin tarayyar Najeriya.
Mohammed Emegu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tattauna da manema labarai a garin Kaduna.
Mohammed, ya ce a matsayinsu na wannan kungiyar suna nan suna gudanar da bincike a kan wannan al’amarin domin gano duk wani mai hannu a cikin wannan lamari domin a hukunta shi ta yadda zai zama darasi ga sauran wadansu a nan gaba.
“Akwai maganganu da yawa a bisa wannan binciken da suka yi, musamman irin abubuwan da suka tattara daga jama’ar da suke a wannan wurin da lamarin ya faru domin wadansu sun ce wai DPO din da ke wanann wurin ne ya bayar da matar, amma kuma a binciken da aka yi a halin yanzu binciken ya tabbatar da cewa wadanda suka taru wato dimbin mutanen da suka taru a wurin sun fi karfin wannan ofishin yan Sanda na Marabar Jos”.
“Kowa ya sani a wannan ofishin yan Sandan ne aka kashe wani DPO na yan Sanda kuma hakan ma ya faru a wani wurin can daban an kashe DPO don haka ne muke cewa da dimbin jama’ar da suka taru fusatattu sai kowa ya tsere har aka samu aka fito da matar aka kone ta. Wanda hakan ba dai- dai bane mun yi tir da faruwar hakan a matsayin mu na kungiya ba za mu bari hakan ta ta fi a banza ba har sai mun ga an hukunta waɗanda suka aikata hakan kuma ba mu amince da hakan ba don haka muna yin kira ga jama’a da duk wanda ya isa da lallai a kama wanda duk yake da hannu a game da faruwar wannan lamarin, tun da dai wani gangami ne na jama’a da yawa don haka duk wanda aka kama su biya duyyar ran wanann matar.
.
“Muna yin kira ne a game da wanann maganar a bayar da diyya domin ya zama wata izina ga wadansu a gobe, domin ba yau ba ne ake aikata irin wannan halin.
Mohammed Emegu ya ce hakika a matsayinsa na shugaban wannan kungiyar sun tausaya wa mutanen Marabar Jos game da irin yadda ake sace masu yara, amma kuma wannan ba dalili ba ne ayi wa wannan mata kisan gilla kamar yadda ya faru a yanzu ba, daga ganin mutum kawai ka kashe shi ba gaira ba dalili, don haka muke yin kira ga Kwamishinan yan Sanda da ya bincika sosai a kuma gabatar da duk mai laifi a kotu in dai an same shi da hannu a wannan lamarin saboda baka zargin mutum sannan a bisa zargi kawai ka yanke masa hukunci wannan ba hukuncin gaskiya ba ne.
“A matsayin mu na musulmi mu masu bin doka ne,don haka muke gaya wa Kwamishinan Yan Sanda lallai duk wanda ke da hannu a wannan abu lallai a hukunta su ko su waye.
Bugu da kari kuma ya dace a fa sani cewa rashin gaskiya ya yi yawa a kasar nan wanda hakan ne ya sa mutane suke kin amincewa da batun Gwamnati saboda zaka ga mutumin da aka same shi da laifi dumu -dumu amma a gobe sai ka gan shi ya na n a waje ya na harkokinsa ba wata matsala, saboda ya na da wani don haka muna nan muna bincike a kan wannan lamarin.
Saboda haka muke shaidawa hukumar Yan Sanda cewa duk wanda aka kama idan aka sake shi bayan ya na da hannu a lamarin idan aka sallame shi to, lallai akwai matsala domin sai mun rubuta takardar koke da korafi a game da hakan don haka a tabbatar an hukunta duk wanda aka kama a wanna lamarin saboda gobe kada su sake aikata hakan.
“Duk da ba a tabbatar da cewa ko DPO ne na Yan Sanda ya bayar da matar ga jama’a ba amma kowa na fadin cewa mutanen da suka fito a wurin nan lallai sun kai kusan dubu Uku don haka meye karfin wannan ofishin Yan Sandan? ai ba su wuce mutane Goma (10) ko ashirin ( 20) ba Yan sandan da ke aiki a wanann ofishin yan Sanda na Marabar Jos to yaya za su yi da mutanen da suka taru? ba za su iya ba kowa ya san hakan, kuma ma mutanen da ake harba masu barkonon tsohuwa suna mayarwa.
“A matsayin mu na kungiya ai mun je munga irin yadda aka lalata wurin don haka muna kan bincike kuma muna shawartar dukkan cibiyoyin da ke da alhakin hakan da su tashi tsaye wajen ganin lallai an bincika an kuma hukunta duk mai hannu a cikin aikata wanann aikin kuma a biya
diyyar wannan matar.

