Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » A Shirye shiryen Aikin Hajji mai zuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kamfanonin Jirage Sama Biyar Don Jigilar maniyata aikin Hajjin 2027
    News

    A Shirye shiryen Aikin Hajji mai zuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kamfanonin Jirage Sama Biyar Don Jigilar maniyata aikin Hajjin 2027

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 13, 20262 Mins Read
    FB IMG 1786651366184
    FB IMG 1786651366184

    Daga Aliyu Samba

    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da amincewar Gwamnatin Tarayya da kamfanonin jiragen sama guda biyar da za su yi jigilar maniyatan aikin hajji na Najeriya a lokacin aikin Hajjin shekarar 2027.

    Read also: Emir of Zazzau Seeks Sustained Efficiency in Hajj Administration*

    Hukumar ta ce an zaɓi kamfanonin ne bayan wani cikakken tantancewa da Kwamitin Tantance Kamfanonin Jiragen Sama ya gudanar, bisa ƙa’idojin tsaro, ƙwarewar gudanar da ayyuka da kuma ƙarfin kuɗi.

    Kamfanonin da aka amince da su sun haɗa da Air Peace Limited, Flynas, Max Air Limited, Saudi Air da UMZA Aviation Services Limited.

    Sai dai NAHCON ta ce amincewar za ta fara aiki ne bayan kammala dukkan yarjejeniyar jigilar maniyatan tsakanin hukumar da kamfanonin, da kuma cika dukkan sharuddan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasar Saudiyya (GACA).

    Read also: DAGA SAUYE-SAUYEN TATTALIN ARZIKI ZUWA WADATA: TINUBU YA GABATAR DA SABON MATAKIN CI GABA, YA SHA ALWASHIN YAƘI DA TALAUCI

    Hukumar ta bayyana cewa za a tsara adadin alhazai da kowane kamfani zai ɗauka da kuma jadawalin tashin jirage tare da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kamfanonin jiragen sama.

    Hukumar ta NAHCON ta kuma ce dukkan kamfanonin da aka amince da su za su gudanar da ayyukansu ne bisa ƙa’idojin Hajjin 2027, ciki har da tabbatar da cewa tikitin jirgin kowane alhaji yana da alaƙa da bayanansa na Nusuk-Masar, tare da bin dukkan ƙa’idojin tsaro da aka gindaya.

    Haka kuma, hukumar ta jaddada cewa kowanne maniyaci zai samu damar ɗaukar kaya mai nauyin kilogram 32 guda ɗaya da kuma ƙaramin kayan hannu mai nauyin kilogram takwas, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka tsara.

    Read also: Just In: Nigeria Secures Additional 10,000 Hajj Slots for 2027.

    NAHCON ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, musamman Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, maniyyata da kamfanonin jiragen sama, da su ba da cikakken haɗin kai domin tabbatar da jigilar maniyatan Najeriya cikin aminci, sauƙi da kwanciyar hankali.

    A cewar hukumar, matakin na daga cikin shirye-shiryen fara aikin Hajjin 2027 tun da wuri domin inganta tsari da hidimar da ake yi i wa alhazan Najeriya.

    aikin hajji jiragen nahcon sama shirin
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGov. Mai Mala Buni A Leader with Proven Grassroots Experience.
    Next Article Babbar Hanyar Sokoto Zuwa Badagry Mai Tsawon Kilomita 1000 Za ta Bunkasa Noma a Arewa – Mohammed Idris

    Related Posts

    News

    JAGA’S ROUTINE: Chairman Jaga Represents Speaker Abbas At Humanitarian Outreach, Receives Community Groups,And Honours Zaria’s Quranic Excellence.

    October 2, 2026
    News

    Zulum Hosts North East Governors in Maiduguri for 13th Forum Meeting

    October 2, 2026
    News

    Engr Jaga Celebrates Rt Hon Abbas Tajudeen at 61 , Commends His Commitment to Zaria and Kaduna State

    October 2, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026315 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026252 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026238 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026178 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026173 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026163 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.