Daga Aliyu Samba
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da amincewar Gwamnatin Tarayya da kamfanonin jiragen sama guda biyar da za su yi jigilar maniyatan aikin hajji na Najeriya a lokacin aikin Hajjin shekarar 2027.
Hukumar ta ce an zaɓi kamfanonin ne bayan wani cikakken tantancewa da Kwamitin Tantance Kamfanonin Jiragen Sama ya gudanar, bisa ƙa’idojin tsaro, ƙwarewar gudanar da ayyuka da kuma ƙarfin kuɗi.
Kamfanonin da aka amince da su sun haɗa da Air Peace Limited, Flynas, Max Air Limited, Saudi Air da UMZA Aviation Services Limited.
Sai dai NAHCON ta ce amincewar za ta fara aiki ne bayan kammala dukkan yarjejeniyar jigilar maniyatan tsakanin hukumar da kamfanonin, da kuma cika dukkan sharuddan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasar Saudiyya (GACA).
Hukumar ta bayyana cewa za a tsara adadin alhazai da kowane kamfani zai ɗauka da kuma jadawalin tashin jirage tare da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kamfanonin jiragen sama.
Hukumar ta NAHCON ta kuma ce dukkan kamfanonin da aka amince da su za su gudanar da ayyukansu ne bisa ƙa’idojin Hajjin 2027, ciki har da tabbatar da cewa tikitin jirgin kowane alhaji yana da alaƙa da bayanansa na Nusuk-Masar, tare da bin dukkan ƙa’idojin tsaro da aka gindaya.
Haka kuma, hukumar ta jaddada cewa kowanne maniyaci zai samu damar ɗaukar kaya mai nauyin kilogram 32 guda ɗaya da kuma ƙaramin kayan hannu mai nauyin kilogram takwas, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka tsara.
NAHCON ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, musamman Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, maniyyata da kamfanonin jiragen sama, da su ba da cikakken haɗin kai domin tabbatar da jigilar maniyatan Najeriya cikin aminci, sauƙi da kwanciyar hankali.
A cewar hukumar, matakin na daga cikin shirye-shiryen fara aikin Hajjin 2027 tun da wuri domin inganta tsari da hidimar da ake yi i wa alhazan Najeriya.

