Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekara 70 da haihuwa.
A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Lahadi, Tinubu ya bayyana Sarkin Musulmin a matsayin jagora mai hikima da kishin zaman lafiya.
Shugaban ya ce shekaru 70 na rayuwar Sarkin Musulmin shaida ne kan rayuwar da ya sadaukar wajen hidima, hikima da jagoranci, musamman tsawon kusan shekaru 20 da ya yi kan karagar mulkin Sarkin Musulmi.
Ya bayyana cewa Sarkin Musulmin ya kasance murya mai tabbatar da zaman lafiya a lokutan tashin hankali, mai hada kan al’umma da addinai, kuma jagora mai bayar da shawarwari ga Musulmi da sauran al’ummar Najeriya.
A cewar Tinubu, Sarkin Musulmin ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ilimi, tattaunawar addinai, ayyukan jin ƙai da zaman lafiya tsakanin al’ummomi, tare da bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kare mutuncin kowane ɗan Najeriya.
Shugaban ya kuma bayyana cewa yana matuƙar daraja haɗin gwiwar Sarkin Musulmi wajen gina ƙasa, musamman a fannonin tsaro, ci gaban al’umma da kuma inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Sarkin Musulmi lafiya, ƙarfi da tsawon rai, tare da kare shi domin iyalansa, masarautar Sokoto da Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma yi fatan wannan shekaru na rayuwar Sarkin Musulmin su kasance mafi alheri da albarka arayuwarsa.
Sabuwar Nigeria

