Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Maulidi: Tinubu ya Bukaci alummar Musulmi su yi koyi da koyarwar Annabi (SAW)
    News

    Maulidi: Tinubu ya Bukaci alummar Musulmi su yi koyi da koyarwar Annabi (SAW)

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 25, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787687410333
    FB IMG 1787687410333

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Maulidin Annabi Muhammad (SAWA), inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayen Manzon Allah.

    A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Shugaban ya ce bai kamata Maulidi ya tsaya kan bikin ranar haihuwar Annabi kawai ba, sai an yi amfani da lokacin wajen yin nazari, addu’a da koyon darussan rayuwarsa.

    Read also: Gov. Yusuf Greets Ooni of Ife on 52nd Birthday

    Tinubu ya ce Musulmi su yi ƙoƙari su riƙa bin koyarwar Annabi Muhammad, yana mai cewa rayuwarsa na ɗauke da manyan darussa na ibada, juriya, haƙuri da sadaukar da kai.

    Read also: Speaker Abbas attracts, commissions two power projects in Soba, lays foundation for others

    Shugaban ya kuma bukaci malaman addini da su yi amfani da lokacin Maulidi wajen yi wa ƙasar addu’a, tare da jan hankalin mabiyansu kan su mayar da darussan rayuwar Annabi a aikace wajen nuna kishin ƙasa.

    Read also: WORLD FOOD DAY: ZAMFARA FIRST LADY PLEDGES TO CONTINUE TO SUPPORT WOMEN FARMERS IN THE STATE

    Haka kuma, ya bukaci Musulmin da ke gudanar da bikin Maulidi su tallafa wa mabukata da masu rauni, musamman a cikin wannan lokaci.

    Shugaban ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da yi wa Najeriya addu’a domin samun nasara kan matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar wasu sassan ƙasar.

    maulid sakon tinubu
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleMAULUD:Governor Yusuf urges Muslims to emulate Prophet Muhammad’s exemplary life
    Next Article Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaro su ceto mutanen da aka sace a jihar Neja

    Related Posts

    News

    Speaker Abbas attracts, commissions two power projects in Soba, lays foundation for others

    October 18, 2026
    News

    Gov. Yusuf Greets Ooni of Ife on 52nd Birthday

    October 18, 2026
    News

    WORLD FOOD DAY: ZAMFARA FIRST LADY PLEDGES TO CONTINUE TO SUPPORT WOMEN FARMERS IN THE STATE

    October 17, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026371 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026343 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026260 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026250 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026194 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026177 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.