Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaro su ceto mutanen da aka sace a jihar Neja
    Security

    Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaro su ceto mutanen da aka sace a jihar Neja

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 25, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787687368775
    FB IMG 1787687368775

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar sojojin Najeriya, da rundunar ‘yan sanda, da Hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri da su fara aikin haɗin gwiwa domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a wani sabon harin satar mutane da ya faru a Jihar Neja.

    A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana matuƙar ɓacin ransa kan sacewa da kashe fararen hula da miyagun masu laifuka suka yi a jihar.

    Read also: Ayarin Jamian Tsaro Na Musamman daga Ofishin mai ba Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro ,NSA Sun Ceto Iyalan Da Aka Sace Da Jaririyarsu A Kaduna

    Shugaban ya ce waɗanda suka kai harin kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, “makiyan zaman lafiya ne kuma makiyan bil’adama”, yana mai cewa ba za a bar su su tsere wa hukunci ba.

    Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe, yana roƙon Allah Ya jiƙansu, Ya kuma bai wa iyalansu ƙarfin jure wannan babban rashi.

    Tinubu ya ce al’ummar da lamarin ya shafa ba su kaɗai ba ne, yana mai cewa ƙasa baki ɗaya na tare da su a cikin wannan mawuyacin hali.

    Read also: Just In: COAS Visits Borno to Boost Troops’ Morale, Assess Operations

    Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta huta ba har sai an dawo da ’ya’ya, iyaye mata da maza da aka yi garkuwa da su cikin aminci.

    Shugaban Ƙasar ya kuma umarci shugabannin hukumomin tsaro da su riƙa ba shi rahoto kai-tsaye kan yadda aikin ceto ke gudana har sai an tabbatar da inda duk mutanen da aka sace suke.

    “Ta’addanci ba zai tsoratar da Najeriya ba. Za mu kare al’ummarmu, mu kare garuruwanmu, kuma mu tabbatar da mutuncin rayuwar ɗan Adam,” in ji shi.

    Read also: NIGERIAN ARMY, DENMARK STRENGTHEN DEFENCE COOPERATION TO ENHANCE NATIONAL AND REGIONAL SECURITY

    Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa addu’arsa na tare da al’ummar Jihar Neja a wannan lokaci na ƙalubale, yana mai cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bai wa gwamnatin jihar dukkan goyon bayan da ake buƙata domin aikin ceto, agaji da ƙara tsaro.

    Sabuwar Nigeria

    agencies direct kidnapped niger pbat rescue security victims
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleMaulidi: Tinubu ya Bukaci alummar Musulmi su yi koyi da koyarwar Annabi (SAW)
    Next Article Governor Radda Announces Personal Funding for Zawiyya Guest House

    Related Posts

    Security

    COAS CHARGES TROOPS IN OPHK TO SUSTAIN OFFENSIVE AGAINST TERRORISTS, ASSURES OF IMPROVED WELFARE

    October 17, 2026
    Security

    Zulum Calls for Coordinated Military Offensive in the Lake Chad

    October 17, 2026
    Security

    COAS HAILS BORNO GOVERNMENT’S SUPPORT, SAYS PUBLIC COOPERATION CRITICAL TO DEFEATING TERRORISM

    October 17, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026371 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026343 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026260 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026250 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026194 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026177 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.