Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Ministan Yaɗa Labarai ya kare rangwamen farashin mai na NNPC, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki za su samar da wadata
    News

    Ministan Yaɗa Labarai ya kare rangwamen farashin mai na NNPC, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki za su samar da wadata

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanOctober 13, 20265 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1791883900599

    Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya kare sauye-sauyen tattalin arziki da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa, da kuma shirin kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC Ltd., na bayar da rangwamen farashin fetur na tsawon kwanaki 30, yana mai jaddada cewa manufar matakin ita ce rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin hauhawar farashin mai ne, ba wai komawa tsarin tallafin man fetur ba.

    Idris ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wata tattaunawa da manyan editocin jaridu da masu gabatar da shirye-shiryen gidajen talbijin da rediyo a Abuja, inda ya amsa tambayoyi kan tsadar rayuwa, alaƙar gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago, wadatar abinci, ababen more rayuwa, tsaro, cin gashin kan ƙananan hukumomi da ’yancin aikin jarida.

    Read also: NPMCN accredits facilities at MAUTH Yola’s for the family medicine department

    Da yake bayanin shirin rangwamen farashin fetur, ministan ya ce kamfanin NNPC ya yanke shawarar yin watsi da wani ɓangare na ribar da yake samu ne domin rage wa ’yan Nijeriya nauyin tsadar mai sakamakon hauhawar farashin makamashi a kasuwannin duniya.

    Ya ce: “NNPC ya duba lamarin, sai ya ce, ‘To, muna samun wannan adadin riba. Me ya sa ba za mu rage wani ɓangare na ribar da muke samu ba domin ’yan Nijeriya su samu wani irin sauƙi?’”

    Ministan ya jaddada cewa shirin ba ya nufin dawo da tallafin man fetur, illa dai wani mataki ne na wucin-gadi da aka ɗauka domin rage wa jama’a nauyin tsadar rayuwa.

    Ministan ya amince da cewa ’yan Nijeriya suna fuskantar matsalolin tattalin arziki, yana mai cewa dole ne sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa su haifar da ingantuwar rayuwar al’umma a zahiri.

    Ya bayyana raguwar hauhawar farashi, ƙaruwa da ajiyar kuɗaɗen waje da kuma bunƙasar kuɗaɗen da ake samu daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba zuwa ƙasashen waje a matsayin wasu alamomin samun cigaba.

    Sai dai ya ce akwai buƙatar tabbatar da cewa talakawa da sauran jama’ar ƙasa sun amfana da wannan farfaɗowar tattalin arzikin.

    Ya ce: “Babban aikin mu a yanzu shi ne tabbatar da cewa wannan farfaɗowar tattalin arzikin da ake gani a manyan ma’aunai ta ƙara bayyana a rayuwar yau da kullum da kuma gidajen ’yan Nijeriya.”

    Game da alaƙar gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago da kuma tsadar rayuwa, ministan ya nuna tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago za su warware matsalolin da suka rage ta hanyar tattaunawa.

    Ya tuna da matsayar Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa ana iya yin bitar tsarin mafi ƙarancin albashi duk bayan shekaru uku maimakon shekaru biyar.

    Dangane da cin gashin kan ƙananan hukumomi ta fuskar kuɗi, Idris ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin wajen aiwatar da tsarin, yana mai cewa ana ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalolin aiwatar da shi da kuma tabbatar da ingantacciyar tafiyar da tsarin.

    Kan batun wadatar abinci, ministan ya ce gwamnati tana tallafa wa noman cikin gida tare da ƙoƙarin ƙarfafa ma’ajiyar abinci ta ƙasa domin inganta samuwar abinci da sauƙaƙa farashin sa.

    Read also: Gov. Radda Assures Traders of Support

    Ya buƙaci ’yan kasuwa da su guji tara kayan abinci domin riƙe su da kuma yin duk wani abu da zai haifar da ƙarancin abinci na ƙarya, yana mai cewa wajibi ne kowa ya taka rawa wajen tabbatar da samun abinci cikin sauƙi.

    “Gwamnati za ta iya samar da abubuwan da za su ba ’yan Nijeriya sauƙi, amma a ƙarshe, ya rage ga ’yan Nijeriya su ma su goyi bayan abin da gwamnati ke yi,” inji shi.

    Idris ya kare ayyukan gina hanyoyin da Gwamnatin Tarayya take gudanarwa, yana mai cewa an tsara su ne domin inganta zirga-zirga, sauƙaƙa kasuwanci, tallafa wa harkokin noma da buɗe sababbin hanyoyin bunƙasa tattalin arziki.

    Ya ce: “Ba a gyara hanyoyi saboda za a yi zaɓe ba. Muna gyara hanyoyi ne domin ’yan Nijeriya su samu damar yin amfani da su, su haɗa birane da juna, tare da samar da hanyoyin bunƙasa tattalin arziki da za su bai wa kasuwanci damar bunƙasa.”

    A kan batun tsaro, ministan ya bayyana cewa an ƙara yawan rundunonin sojojin da ke gudanar da ayyukan soja daga takwas zuwa 12, tare da inganta tallafin da ake bai wa jami’an tsaro.

    Ya amince da cewa har yanzu ƙasar nan tana fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, amma ya sake jaddada aniyar gwamnati ta ƙarfafa tsarin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

    Da yake mayar da martani kan damuwar da aka nuna game da ’yancin aikin jarida da rahotannin kama mutanen da ke bayyana ra’ayoyin su na siyasa, Idris ya ce bai san da wani umurni da Shugaba Tinubu ya bayar na danne kafafen yaɗa labarai ba.

    Sai dai ya yi alƙawarin neman ƙarin bayani kan takamaiman abubuwan da ’yan jaridar suka gabatar yayin tattaunawar.

    Ministan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su kiyaye ƙa’idojin aikin jarida, su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su, sannan su guji kanun labarai masu ruɗarwa ko ƙara gishiri a cikin labari.

    Ya jaddada cewa ’yancin aikin jarida dole ne ya kasance tare da ɗaukar nauyin da ke tattare da shi.

    “’Yancin aikin jarida ba wani abu ba ne da yake rataye shi kaɗai a sararin samaniya. Akwai wani abu da yake tare da shi, wato nauyin da ke kan waɗanda suke amfani da wannan ’yanci,” inji shi.

    Read also: Governor Radda Inspects APC Secretariat Under Construction in Katsina

    Idris ya yaba wa kafafen yaɗa labaran da suka halarci taron bisa yadda suka shiga tattaunawar, yana mai bayyana shirin sa na ci gaba da irin wannan zaman, mai yiwuwa a kowane mako biyu.

    Ya ce gudanar da tattaunawar a kai a kai zai ƙarfafa sadarwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kafafen yaɗa labarai, tare da samar da damar fayyace manufofin gwamnati da tattauna batutuwan ƙasa da ke tasowa.

    FB IMG
    FB IMG 1791883910648
    FB IMG
    FB IMG 1791883905246
    FB IMG
    FB IMG 1791883894967
    fg Idris kare matsayin ninista ya
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGovernor Radda Inspects APC Secretariat Under Construction in Katsina
    Next Article Shettima ga Arewa: Kada ku damu, babu abin tsoro a wa’adin Shugaba Tinubu na biyu

    Related Posts

    News

    Gov. Radda Assures Traders of Support

    October 13, 2026
    News

    Shettima ga Arewa: Kada ku damu, babu abin tsoro a wa’adin Shugaba Tinubu na biyu

    October 13, 2026
    News

    Governor Radda Inspects APC Secretariat Under Construction in Katsina

    October 13, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026335 Views

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026302 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026259 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026249 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026194 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026177 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.